Connect with us

MANYAN LABARAI

Alhakin Ta’addanci A Zamfara Yana Kan kungiyar ‘Yan-sa-kai Ne—Gwamnatin Jihar

Published

on

Kwamishinan tsaro da harkokin cikn gida na jihar Zamafara Hon. Abubakar Mohammed Dauran ya ce, dukkan hare-haren da Fulani ke kaiwa a jihar hare-hare ne na ramuwar gayya, na harin daka kai musu a baya.

Kwamishinan ya bayyana haka a tattauwarsa da ‘yan jarida a ofinshinsa dake Gusau, yana mai cewa, lallai komai yana ne faruwa ne tare da dalili.

”Ban taba ganin inda aka samun zaman lafiya ba tare da adalci ba a dukk duniya,” inji shi.

”Al’umma Fulami a jihar Zamfara sun fuskanci komawa baya da wulakanci, akan haka suka kasance cikin haushi da kunci ”

Ya kuma ce, hari da aka kai na baya-baya na a yankin Dansadau, hari ne na ramuwar gayya don kuwa ‘yan kungiyar Yan-sa-kai sun kashe wani Bafulatani tare da kwashe musu mashin, yayin da daya ya tsira da kyar a harin.

Ya kuma lura da cewa, ‘yan kungiyar Yan-sa-kai sun dade suna gallaza wa al’umma saboda goyon bayan da suke samu daga gwmanatin tsohon gwamna Abdula Aziz Yari, suna sace wa Fulani shanayen su haka yake sawa Fulanin ke kai harin ramuwar gayya.

Kwamishinan ya kuma ce, babu yadda Fulani za su kai wa al’umma hari ba tate da an kai musu hari ba, ya kuma kara da cewa, yan kungiyar ‘Yan-sa-kai sune babbar matsalar jihar a bangaren tsaro a halin yanzu.

”A kan haka wanna gamnatin ta Bello Matawalle ta amince da cewa, bindiga da harshasai kadai ba za su iya kawo karshe wannan ayyukan na ta’addanci a jihar ba ”

”Dole gwmanatin jihar ta bayar da karfi wajen kawo karshen kungiyar ‘yan-sa-kai ta haka za a tatabbar da samar da zaman lafiya a jihar”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: