CRI Hausa" />

Alhamis Ba A Samu Sabon Wanda Ya Harbu Da Cutar COVID-19 A Babban Yankin Sin Ba

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta ce a dukkanin babban yankin kasar Sin, ba a samu ko da mutum daya, da ya harbu da cutar COVID-19 a ranar Alhamis ba.

Hukumar wadda ta yi wannan tsokaci a yau Jumma’a, ta ce mutane 39 da aka samu dauke da cutar a ranar, dukkanin su sun shigo da ita ne daga ketare.
A wani ci gaban kuma, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da cewa, rashin sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin, babbar nasara ce da aka cimma. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)

Exit mobile version