Alhazan Jihar Bauchi Sun Fara Dawowa

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A karon farko, jirgin alhazan Jihar Bauchi ya fara dawowa daga kasa mai tsarki dauke da alhazan Jihar Bauchi kimanin su 295, daga cikin adadin na alhazan mutum hudu daga cikin ma’aikatan hukumar jin dadin alhazai ne a yayin da sauran adadin kuma dukkaninsu alhazan Jihar Bauchi ne.

Kamfanin jigilar alhazai na ‘Flynas’ ne ya kawo alhazan daga Jidda inda suka iso Bauchi da misalin karfe 4:45 na yamma. Alhazan sun fara dawowa ne a jiya Talata bayan da suka yi nasarar gabatar da ibadunsu na aikin hajji a cikin wannan shekarar na 2017. Ana sa ran alhazan Jihar Bauchi za su ci gaba da dawowa gida ba tare da samun tangarda ba.

A wani labarin kuma, kimanin alhazan Jihar Bauchi su uku 3 ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da suke kan aiyukan ibadarsu na aikin hajji a wannan shekarar 2017. Alhazai biyu daga karamar hukumar Shira wadanda suka rasu a kwanakin baya a sakamakon rashin lafiya, a yayin da wani alhajin shi kuma ya rasu a ranar lahadin nan da ta gabata a sakamakon ciwon zuciya.

Da yake tabbatar da rasuwar na Alhazan jami’in lafiya na hukumar jin dadin alhazan jihar Bauchi Muhammad Dan Azumi Haladu ya ce alhazai biyu da suka rasu dukkaninsu sun fito ne daga karamar hukumar shira a yayin da kuma wani alhazan ya sake rasuwa a ranar lahadin da ta gabata “Shi wannan alhazan jihar Bauchi ne amma ya biya ne daga ofishin hukumar alhazai, alhazan wanda ciwon zuciya ya kashe san, zai iya kaiwa shekaru 55. Ya rasu ne a sakamakon ciwon day a damesa nina kaisa asibiti ana kokarin duba lafiyarsa daga baya rai yayi halinsa”. In ji sa

Jami’in lafiyar ya shaida cewar ya zuwa yanzu dai alhazan jihar Bauchi suna ci gaba da samun kulawa sosai ta fuskacin kula da lafiyarsu da kuma kiwon lafiyarsu ya bada tabbacin cewar shirye shiryen dawow da alhazan jihar Bauchi gabaki dayansu ma ya yi nisa.

Mamba a kwamitin jin dadin alhazan jihar Bauchi Shaikh Isma’il Bajoga ya shaida cewar dawowar alhazan jihar Bauchi ne yanzu suka nufa suke kuma kai, ya bayyana cewar alhazan jihar Bauchin za su dawo ne a jere “Dukkan tsarin da aka yi suna jere kuma suna tafiya daidai, insha Allahu alhazan jihar Bauchi za su ci gaba da dawowa ne a jere. Babu jinkiri, ana kan diban kayan alhazai ma”. In ji shi

Exit mobile version