Connect with us

MANYAN LABARAI

Alhazan Jihar Kaduna 1,494 Sun Dawo Gida

Published

on

Hukumar alhazan jihar Kaduna ta ce alhazan jihar 1,494 ne daga cikin alhazai 3,238 suka samu isowa gida daga kasar Saudiyya bayan kammala ayyukan hajjin bana.

‘Kimanin alhazai 318 sun dawo ne a jirgin saman kamfanin Medview a yau Asabar, inda sauran kuwa suka dawo cikin wasu jiragen daban, muna sa ran kwasu sauran alhazan cikin tsari nan ba da jimawa ba.’ inji kakakin hukumar

Kakakin ya kara da cewa: duk alhazan jihar Kaduna mun baiwa ko wannensu lita biyar na ruwan Zamzam, sannan kowa zai je sansanin alhazai na jiha da ke Mando don ya karbi kayanshi da ya yi tsaraba daga kasar Saudiyya.
Advertisement

labarai