Daga Abubakar Abba, Kaduna
Mai lura da Hukumar alhazai reshen Jihar Kaduna Imam Hussaini Sulaiman Tsoho, ya tabbatar da rasuwar mahjjata uku da suka fito daga jihar yayin aikin Hajjin da ya gabata a kasa mai tsarki.
Jami’in ya ce, alhazai biyu sun rasu ne kafi hawan Arfa, yayin da dayan kuwa ya kamu da rashin lafiya a ranar Arf wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa bayan kwana biyu a wata asibitin Makka.
Kazalika ya bayyana cewa, an samu wasu alhazai biyu da suka yi targade aka kai su asibiti bayan sun samu sauki aka sallame su.
A karshe, jami’in ya ce, kimanin alhazai dari bakwai ne daga jihar suka sauke faralinsu a Bana, inda adadin ya wuce yawan kujerun da Hukumar Alhazai ta Kasa ta ware wa jihar.