Daga Umar Faruk, Birnin, kebbi
Rahotannin da dake fitowa daga Saudiyya zuwa Jihar Kebbi sun nuna cewa Alhazan jihar ta Kebbi mutum hudu ne suka rasu a kasa mai tsarki.
Wadannan mahajjata hudu sun rasu saboda gajeruwar rashin lafiya da suka yi fama da ita asibitin kasar saudiya. Biyu daga cikin hudu suka Rasu a asibitin garin Makkah, Saudi Arabiya.
Alhazan da suka Rasu sun had a da matar shugaban karamar hukumar mulki ta Shanga Hajiya Rashida Yusuf Musa daga Shanga, Fati Adamu Fakkai karamar hukumar mulkin Argungu, Adamu Liman Suru karamar hukumar mulki ta Suru da kuma babban malamin islama a karamar hukumar mulki ta Zuru , malan Sani Haruna Zuru.
Dakta Hali Bala Wanda ya bayyana Rasuwar Alhazan hudu a wata hira da ya gudanar ta harshe hausa ga manema labaru na jihar ta kebbi da ke kasar saudiya domin aiko rahotanin a jihar kan aikin hajjin na bana.
Wanda ya kasance mamba na kwamitin Amirul Hajj na jihar kebbi a karkashin jagorancin Sarkin Zuru, Alhaji Sani Sami, Gomo na biyu, don aikin Hajjin na Nana.
Bugu da kari yace, ya samu wannan labarin rasuwar alhazan hudu ne daga bakin shugaban hukumar kula da jin dadin alhazan jihar kebbi Alhaji Bala Musa Sakaba, kuma yace Alhazan hudu suka fito ne daga kananan hukumomi na mulki daban daban na jihar ta Kebbi.
Wakilin gidan talabijin na jihar ta kebbi Muhammad Tukur Umar shine ya samu zatawa da Dakta Hali Bala a kasar Saudi, inda ya ruwai toshi a cikin rahotannin da ya aiko a gidan talabijin na jihar ta kebbi, yana sanar war Rasuwar Alhazan hudu a labarin karfe 7 na yamman jiya , wanda Yahaya Muhammad Gwandu ya karanto labarun ta harshen hausa kuma ya ruwaito muryar wakilin su daga makka .
Daga nan Dokta Hali ya kori iyalan Alhazan hudu da kuma ‘yan uwan su da dauki dangana kuma su yadda da cewa kowa ce rayuwa sai ta dandani mutuwa .
Yace zasu yi amfani da wannan dama ta mika gaisuwar ta’aziyar su ga iyalan Alhazan da suka Rasu. Ya bukaci iyalai suyi imani da kuma suyin hakuri na rasa ‘yan uwa. Hakazalika ya yi addu’a ga Allah da ya rahamshe su ya gafarta mu.