Daga Sharfadeen Sidi Umar, Sakkwato
Hukumar Alhazzan Jihar Sakkwato ta bayyana alhini da jimamin rasuwar mahajjatan jihar biyu a Birnin Makka, Kasar Saudiya.
Alhazan wadanda suka karbi kiran mahalaccinsu su ne Luba Usman daga Karamar Hukumar Illela da kuma Musa Haruna daga Karamar Hukumar Gada.
Ibrahim Umar Shugaban Hukumar Alhazan Jihar Sakkwato ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai.
Da yake bayanin yadda suka rasu daya bayan daya, Umar ya bayyana cewa gabanin rasuwar ta Luba Usman ta na cikin koshin lafiya, ta gamu dakarar kwana ne a lokacin da take kalacin safe a inda ta fadi ta ce gagarin ku nan. Musa Haruna kuwa, Shugaban Hukumar ya bayyana cewa kafin rasuwarsa yana cikin Alhazan da za su dawo Nijeriya a cikin jirgin farko naMahajjatan Karamar Hukumar Gada. Ya ce lamarinta ya auku lokacin da suke cikin layi a daren Asabardomin auna karamar jakar hannu a yayin da karin kwana ya riske shi.
Shugaban Hukumar ya bayyana cewa an yi jana’izar marigayan bayan an yi masu sallah a masallacin Harami a Makka. Ya kara da cewar jirgin farko na Alhazan jihar Sakkwato ya dawo gida a daren Lahadi da Alhazai 550 daga Kananan Hukumomin Gada da Sabon Birni. Ya ce, jirgi na biyu zai bar filin jirgin saman Sarki Abdul’aziz da ke Jidda zuwa Sakkwato a ranar Litinin da karfe 11 na dare dauke da Alhazai 520.