Hukumar ‘yan sandan Jihar Kano ta gayyaci Ali baba, mai baiwa Gwamnan Kano shawarwari a kan harkar addini bisa zargin da Ali baba ya jinginawa Kwankwaso na mallakar Kamfanin Dangote Oil a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo a Kano.Inda da kyar aka bayar da belinsa bisa sharadin komawa gidan rediyon ya karyata kansa da kansa, kuma sai da yayi hakan. Inji majiyar.
A tattaunawar, Ali baba ya bukaci Kwankwaso ya fito fili ya yi rantsuwa a kan cewa ba kamfaninsa bane. A cewar Ali Baba, kalar kamfanin ja da fari ne, kuma hakan yabyi kama da kalar da kwankwaso yake amfani da ita a siyasarsa.
Ali Baba, wankda kuma shi ne hadimin Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi UmarGanduje kan harkokin addini, ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha a kan wannan al’amari.
Ma’aikatan Kamfanin Aliko Oil sun hassala da wannan magana ta Ali Baba, inda suka kai karar Ali Baba shelkwatar ‘yan Sanda ta Kano da ke Bompai.
A ranar Asabar data gabata, Alibaba ya bayyana a shirin gidan rediyon, ya baiwa kamfanin hakuri bisa alakantasu da tsohon Gwamnan da ya yi.
Da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna, cewa ya yi ba shi da labari a kan faruwar lamarin, saboda ya yi tafiyar ‘yan kwanaki. Kamar yadda Daily Nigeria ta rawaito.