Idan mace ta wayi gari tana yawan mafarki wani na saduwa da ita cikin bacci si ake kira aljanin namijin dare, kasancewar yadda wannan al’amarin ya yi yawa a tsakanin mata kuma har ya kai ga wasu cututtuka suna faruwa ga mace ko namiji ko kuma cututtukan da ba sa jin magani a yi ta wahala har a gaji. Shi ya sa na ga ya dace in kawo wannan bayani domin samar da mafita a kan waxannan matsaloli.
Dalilin Samuwar Namijin dare wanda ake ce masa Jinnul Ashik da Larabci.
Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur’ani da Sunnah, kamar cikin Majmu’ul fatawa na Shaikul Islam ibnu Taimiyyah da
littafin Ash-shifa’u bil qur’an minal jinnu wash shayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul qur’an li’ilaj as-hir wal massi as-shaixani suka ce:
Wannan Aljani da ake kira jinnul Ashik yakan samu mace ta hanyoyi hudu kamar haka:-
1: Wata shi yake kawo kansa saboda rashin kyautata sutura da shigar banza na kayan zamani, wanda musulunci ya hana.
2: Wata kuma ita take kai kanta inda aljanun suke, kamar zuwa wajen bokaye.
3: Wata kuma sihiri aka yi mata saboda ta hada nema da wani maras tsoron Allah.
4: Wata kuma tana kyautata sutura, tana bin Allah, amma Allah zai jarrabe ta da wannan shaidani.
A takaice dai wadannan hanyoyin da shi wannan shaidani zai zo wajen ta sai ya mayar da abin ya
koma zuwa soyayya ya raba ta da kowa ya hanata yin aure ko ya rabata da mijinta ko ya hanata zaman lafiya da shi, shi kuma Aljanin ya ci gaba da zama da ita yana saduwa da ita ya dauke ta kamar matarsa kuma ya hana mijinta
komai da ita, ya sa gaba da kiyayya a tsakani. Allah ya kiyaye.
Hanyoyin Da Yake Bi Ya Zo Wa Mata A Matsayin Mijin Dare Su Ne kamar Haka
1: Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wadda take jin kunya ko wadda bata sani ba ko dan uwanta ko ta siffar mace ‘yar uwarta.
2: Yakan zo mata a siffar mijinta yana saduwa da ita a zahiri ba a mafarki ba, amma kuma shaidani ne ba mijinta ba ne.
3: Yakan zo wa mace tana kwance ta ji kamar ana saduwa da ita, ita ba mafarki ba, ita kuma ba idon ta biyu ba.
4: Wata macen ta kan kwanta ta yi barci ba wadda ya sadu da ita, amma idan ta farka ta wayi gari sai ta ga kamar wani ya sadu da ita.
Alamomin Namijin Dare
Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar shi ne:-
Shi wannan shaixanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayin, amma sai su xauka shirmen mafarki ne kawai, to a gaskiya ba haka ba ne.
Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da waxannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta
waxannan matsalolin za ta ce maka tana fama da su. Daga ciki akwai:-
1: Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake ta, ta gaji da auren, da za ka tambaye ta laifin mijin ba za ta faxi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar ‘yan’yanta.
2: Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma ba ya jin magani.
3: Tsananin ciwon qirji da ciwon baya.
4: Tsananin ciwon mara lokacin al’ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace, shi ba al’ada ba ne, kuma ya kasu kashi 2; mai yauqi da maras yauqi ko mai kauri kamar koko tare da yawan qaiqayi ko fitowar quraje.
5: Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki, amma za ta iya kasancewa ta dauki alamomi na masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan mafarki ta haihu.
6: Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita ba zafi, amma ba ta samun biyan buqata.
7: Daf da magariba ta dinga jin zazzavi ko faxuwar gaba ko yawan tsorata, ko kasala da vacin rai.
8: Idan ta xauki Alku’ani za ta karanta sai ta dinga jin kasala da hamma da hawaye da barci da zarar ta ajiye kur’anin sai ta ji wartsake kamar ba ita take jin bacci ba.
9: Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin bacci sai ta kasa, ta yi ta juyi ta kasa bacci, mijinta na zuwa kusa da ita sai ta dinga samun firgita da tsoro.
10: Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kaxewa ko ya yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko ya yi ja.
11: Yawan qaiqayin ido da qaiqayin kai na amosani, amma ba amosani ba ne.
12: Yawan kaikayin kunne da yawan kaikayin hanci kamar mura, amma ba mura bane, ko yawan kumburin ciki.
13: Yawan zubar jini da ba na al’ada ba, ko jinni ya riqa yi mata wasa. Sannan kuma har ma wacce ba ta da aure
budurwa ko bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita bambancin da ke tsakani da ita wacce take da aure shi ne kamar haka:-
1 Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.