Aljeriya Ta Lashe Gasar kofin Nahiyar Afrika Ta 2019

A yau ne a doka wasan karshe tsakanin kasar Senegal da Aljeriya a gasar kofin Nahiyar Afrika na shekarar 2019 wanda a buga a kasar Masar. Aljeriya ta lashe gasar ne bayan doke takwarar ta kasar Senegal da ci daya mai ban haushi.
Dan wasan Aljeriya Baghdad Bounedjah ne ya jefa kwallo daya tilo a cikin wasan a minti na biyu da fara wasa
Wannan shine karo na biyu da Aljeriya ta lashe wannan kofin. Ta lashe na farko shekaru 19 da suka wuce yayin da kawo yanzu Senegal bata taba lashe kofin gasar ba.

Exit mobile version