Alkalai Sun Yanke Hukunci Dubu Dari Cikin Shekara Guda A Adamawa

Alkalai

Daga Muh’d Shafi’u Saleh,

Alkalan kotuna na bangaren shari’a a Jihar Adamawa sun yanke hukunci kan aikata miyagun laifuka da wasu sama da dubu dari (100,000) cikin shekara guda.

 

Mukaddashin babban mai shari’a a jihar, Mai Shari’a Nathan Musa, ya bayyana haka da yake jawabi a bikin ranar shari’a ta 2021/2022 da ya gudana a Yola. Ya bayyana cewa sashin shari’ar ya samar da kudin shiga sama da naira miliyan 6 a shekarar.

 

Mai shari’a Nathan Musa, ya ce an dauki bayanai shari’o’in ne a kotunan yankunan, kotunan majistire, manyan kotunan yankuna da babbar kotunan jihar.

 

Ya ci gaba da cewa “Cikin wadannan shari’o’i dubu 100, mun sallami dubu 70, mun kuma samar da naira miliyan 6, a matsayin kudaden shiga na jiha.

 

“Mun samar da kudaden ne daga tara, shigar da shari’o’i da sauran rantsowar da ake yi” in ji Nathan Musa.

 

Da yake magana kan walwala da jindadin ma’aikatan bangaren shari’a kuwa, Nathan Musa ya ce an sabonta batun biyan kudaden jinyar ma’aikatan da biyan kudaden hutu wanda kowa yanzu ya san an sabonta wannan.

 

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yaba wa mukaddashin babban mai shari’a Nathan Musa, bisa inganta bangaren shari’ar wanda lamarin ya dawo da martaban sashin.

 

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Crowther Seth a warin bikin,  ya ce wannan taro bai  zama na tarihi ba kawai ga bangaren, tarihi ne ga jihar baki daya.

 

Haka kuma gwamnan ya yaba wa babban mai shari’an kan inganta walwala da jindadin ma’aikatan, ya ce gwamnatin jihar za ta yi duk abin da ya kamata domin samun nasarar sashin shari’ar.

 

Kwamishinan shari’a, Afremu Jingi ya yaba da gyara fannin shari’ar da mukaddashin babban mai shari’ar ya yi, musamman a tsarin gudanarwar kotunan yankuna.

 

Ya ce “Duk gyare-gyaren da ya shaida mana suna da inganci a sashen shari’a kuma muna tabbatar maka za mu yi duk abin da ya kamata wajen tabbatar da ganin an cimma nasara” in ji Jingi.

Exit mobile version