Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jose Mourinho, ya ce jami’an kula da wasanni basu yi masa adalci ba, yayin wasan gasar Premier da kungiyarsa tayi rashin nasara a hannun zakarun gasar wato Liverpool da 2-1.
Mourinho na korafi ne kan yadda jami’ai da alkalan wasa suka ki goyon bayansa yayin da yake cacar baka tsakaninsa da kocin Liverpool Jurgen Klopp, wanda ya nuna murna kan kwallo ta biyu da dan wasansa Roberto Firmino ya ci a mintuna na 90.
Sai dai salon nuna murnar da Klopp yayi amfani da shi bai yiwa Mourinho dadi ba, wanda ya ce inda shi ne yayi hakan to babu mamaki a dauki matakin ladabtarwa a kansa saboda a baya ansha yi masa irin wannan hukuncin.
Mourinho ya kuma caccaki kocin Manchester City Pep Guardiola kan yadda a ranar Talata yayin wasan da suka tashi 1-1 da West Brom, kocin yayi kokarin hana mataimakin alkalin wasa daga allon dake nuna karin lokaci na mintuna 4 a wasan, dabi’ar da Mourinho ya ce da shi ne yayi, da tuni an kore shi daga fili.
Yanzu haka dai Tottenham dake fatan lashe kofin gasar Premier na farko cikin shekaru 60, na matsayi na 2 a gasar da maki 25, biye da Liverpool a matsayi na daya da maki 28 sai Southampton a matsayi na uku sai Leceister City a matsayi na hudu Eberton ta biyar sai kuma Manchester United a matsayi na shida.