Balarabe Abdullahi" />

Alkali Kuliya Manta Sabo Ya Daure Boka Da Dan Rakiya A Zariya

Yanzu haka dai babbar kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci da ke Tudun Wadan Zariya bisa jagorancin alkalin kotun, Alhaji Nuhu Mahmud, ta yanke hukumcin daurin shekara uku ga wani boka da kuma wani wanda ya je wajensa, domin neman maganin rufe bakin abokin shari’a, tare da dan rakiyarsa.

Tun farko dan sanda mai gabatar da wadanda a ke zargi da aikata laifuffuka a gaban wannan kotu, Abdulhamid Sarki ya shaida wa Alkalin kotun cewar, mutum na farko day a gabatar a kotun shi ne wani mutum mai suna Ibrahim Barau, da ake zargi da zuwa wata makabarta a garin Farin Kasa ta karamar hukumar Soba, da daddare, inda ya sa danyen kwai a cikin wani sabon kabari.

Da ya je ga hannun ’yanda, a cewar dan sanda mai gabatar da wadanda a ke zargin aikata wasu laifuffuka, ya ce wani boka ne ya ba shi wannan danyen kwai, ya sa a cikin kkabari, domin neman maganin rufe bakin wani mutum da ya ke shari’a da shi, wato wannan kwai, a cewarsa, shi ne zai zama silar rufe bakin abokin shari’arsa.

Shi kuma bokan mai suna Auwal Abubakar, ya ce, tabbas, ya ba Ibrahim Barau wannan kwai ne, domin ganin abokin shari’arsa bai sami damar yin magana ba a gaban alkali, a wata shari’a da ya ke yi da wani abokin shari’arsa.

Dan sanda mai gabatar da wadanda a ke zargi a gaban wannan kotu ya kara da cewar, sai mutum na biyu mai suna Ahmadu Ahmad, wanda ya raka Ibrahim Barau zuwa makabarta domin sa kwai, kamar yadda wannan boka ya umurce shi da ya yi, ya tabbatar wa ‘yan sanda cewar lallai da shi a ka je wannan makabarta domin sa kwai a cikin kabari.

Bayan dan sanda mai gabatar dawadanda a ke zargi da aikata wannan Abdulhamid Sani ya kammala yi wa Alkali Alhaji Nuhu Mahmud bayanin wadanda a ke zargi, sai ya juya ga wadanda a ke zargi, inda dukkansu su ka yi wa alkali bayani tare da amsa laifinsu, wato Ibrahim Barau dan shekara 50 da haihuwa, ya ce, lallai ya karbi kwai a wajen Auwal Abubakar (Boka) tare da umartar sa da ya je makabarta ya sami sabon kabari ya cusa wannan kwai a ciki.

Shi kuma Ahmadu Ahmad, dan shekara 55 ya tabbatar wa Alkali cewar, ya raka Ibrahim Barau makabarta, domin ya cusa kwan a cikin sabon kabari, kamar yadda boka ya umarta.

Bayan Alkali Mahmud ya kammala jin bayanin wadanda a ke zargi tare da dukkaninsu su ka amince da zargin da a ke yi ma su, a nan take Alkali ya yanke wa Boka Auwalu Abubakar, dan shekara 25, da Ibrahim Barau, wanda ya cusa kwai a sabon kabari, daurin shekara uku kowannensu su biyu ko kuma tarar Naira 150,000.

Shi kuma dan rakiya zuwa makabarta, Ahmadu Ahmad, alkali ya daure shi wata biyu ko tarar Naira 30,000.

Bayan kammala bayyana hukumcin sai Alkali Nuhu Mahmud ya nuna matukar damuwarsa da yadda al’umma a yau suka rungumi saba wa Allah da kuma cutar da al’umma. Wannan, a cewarsa, na daga cikin matsaloli daban–daban su ka dabaibaye al’umma, kuma suka zama silar rasa rayukan al’umma dare da kuma rana, a karshe, sai ya yi kira ga al’umma da a yi karatun ta natsu, domin kawo karshen matsalolin da su ke durkusar da al’umma, yayin da wasu kuma suke rasa rayukansu.

Exit mobile version