A shekaran jiya Alhamis ce, mai jagorar shari’ar tsohuwar Shugabar Ma’aikata, Winifred Oyo-Ita, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi barazanar janyewa da ci gaba da sauraren karar.
Ms Oyo-Ita, wacce ta yi ritaya ba tare da wani bata lokaci ba, saboda zarge-zargen da ake yi mata da suka shaficin hanci da rashawa a karshen shekarar 2019, an gurfanar da ita ne tare da wasu a gaban Alkali kan badakalar kudaden da suka kai Naira milyan 570.
Taiwo Taiwo, Alkalin kotun, ya fusata cewa masu gabatar da kara sun yi biris da umarnin da ya bayar na dakatar da shari’ar da aka gabatar a kan wasu mata uku da aka gurfanar da Misis Oyo-Ita a gaban wani Alkali.
Shari’ar wacce ta yi daidai da ita, ita ce takardar neman kwacewa ta wucin gadi da mai gabatar da kara ya gabatar a gaban Folashade Giwa-Ogunbanjo, mai shari’a Babbar kotun Birnin tarayya dake a Abuja, don dakatar da asusun wadanda ake zargin su tare.
“Yi abin da ake bukata ka cire shi, in ba haka ba zan mayar da fayil zuwa ga Babban Alkali.
“Ba zan iya zartar da umarnin da wata ‘yar uwa kotu ta bayar ba,” Haka Mista Taiwo ya yi kashedi a ranar Alhamis.
Ranar 1 ga Disamba, na shekarar 2020, lauya ya bayyanawa Mista Taiwo cewa Hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa tu’annafi (EFCC) cewar da gangan ne ta samu umarnin dakatar da asusun abokan huldar su daga wani Alkalin, Folashade Giwa-Ogunbanjo.
Da yake bayyana ci gaban a matsayin “cin zarafin tsarin kotu,” mai gabatar da kara ya bukaci kotun da ta dage ci gaba da sauraren shari’ar har abada, har sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gabatar da shaidar cewa asusun ba a bude shi ba.
Alkalin, wanda bai gamsu da hujjojin EFCC ba, bayan sauraren lauyoyin da suke kare mai laifin, ya ce matakin da mai gabatar da karar ya dauka wani abinda bai kamata bane, da kuma nuna rashin amincewar hukumar a kotunsa.
Manema labarai sun bayyana cewa Mista Taiwo ta bayyana a ranar a ranar Alhamis cewa, a ranar 3 ga Disamba 2020, ya umarci lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, da ya rufe shari’ar dake wata kotun.
Ya ce ya dage sauraren karar har sai zuwa ranar 13 ga watan Janairun wannan shekarar, amma har yanzu bai samu komai ba daga cikin abubuwan da za su taimaka masa,kuma suke nuna cewar EFCC ta dauki matakai a wannan bangaren.
Ya cigaba da bayanin“Me ya sa za ku ce Ogunbanjo Alhalimai shari’ar shari’ar tana nan haka dai ya kara yin tambaya ranar.
Da yake mayar da martani, lauya mai shigar da kara, Mista Abubakar, ya ce EFCC ta shigar da karar ne don ta samu umarnin dakatar da asusun, amma Babban Alkalin kotun ne ya ya kawo cikas.
Ya nace cewa dole ne mai gabatar da kara ya dakatar da shari’ar a gaban Ms Giwa-Ogunbanjo, Mista Taiwo ya ce, “Wannan shi ne abin da doka ta bayyana.”
“Za mu ga yadda za mu iya janye shi,” in ji Abubakar a cikin shi tsarin shari’ar.
Daga nan sai Mista Taiwo ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu. Baya ga Misis Oyo-Ita, sauran wadanda ake karar sun hada da, Frontline Ace Global Serbices Ltd da Asanaya Projects Ltd, Garba Umar, da kuma kamfanoninsa guda biyu, Slopes International Ltd da Gooddeal Inbestment Ltd – na 2 zuwa na 6.
Wadannan su ne na 7 zuwa na 9 da ake tuhumar su ne, Ubong Okon Effiok, da kamfanoninsa guda biyu, U & U Global Serbices Ltd da Prince Mega Logistics Ltd.
Hukumar ta EFCC ta zargi tsohuwar shugabar ma’aikatac ta kasa, da aikata zamba cikin aminci dangane da alawus din sa, alawus-alawus, kudaden da ake karba na cin hanci a cikin ita kwangilar.
Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja
Daga Sulaiman Ibrahim Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, alkalin kotun koli...