Daga Khalid Idris Doya
Alkalin Kotun Majistire da ke Abuja, Ibrahim Mohammed ya umarci a cafke tare da sanya mari wa wani Lauya mai suna Barista Eburru Ekwe Barth, bisa kalubalantarsa da ya yi a lokacin zaman kotun kan wani karar da ke gaban kotun.
Alkalin kotun Majisire lamba 2 da ke Wuse Zone 6, a Abuja daga nan kuma ya daure Barista Ekwe tsawon watanni biyu a gidan yari bisa shishshigi da raini wa kotun.
Lauyan bayan umarnin na Alkalin, ‘yan sandan da ke aiki a kotun sun sanya masa mari tare da yin awon gaba da shi ba tare da bata wani lokaci ba.
Wani Lauyan da ke cikin kotun ya shaida wa majiyarmu cewa laifin da kotun ta samu Barista Ekwe Barth da shi, shi ne ya tsoma baki tare da yin katsalandan wa Alkalin lokacin da ke yanke hukunci kan wani bukata da Lauyan da ke adawa da shi kan shari’ar ya shigar a gaban kotun.
Dalilin tsoma bakin Lauyan shi ne ya nuna cewa Alkalin ya jingina wani batun da shi sam bai taba fada ba a yayin yanke hukuncin. Nan take Lauya Ekwe ya tambaya a bayyanar kotun cewa shin ko akwai hadin baki ne a tsakanin Alkalin kotun da Lauyan masu shigar da kara.
Tsoma bakin Lauyan yayin wannan hukuncin, ya fusata Alkalin matuka gaya wanda hakan ya sanya shi bada umarni nan take na a cafke masa Lauyan tare da daure shi bisa shishshigi da tsoma baki ga kotun.
Lauyoyin da suke cikin kotun da dama sun yi ta rokon Alkalin da ya sassauta gami da dage kafa wannan hukuncin nasa amma ya sanya kafa ya shure rokon nasu. Tuni dai aka wuce da lauyan zuwa gidan yarin Suleja bayan cafke shi.