Connect with us

RIGAR 'YANCI

Alkalin Alkalan Kogi, Mai Shari’a Ajanah, Ya Rasu

Published

on

Da sanyin safiyar jiya Lahadi ne, Allah ya yi wa Alkalin Alkalan Jihar Kogi, Mai Shari’a Nasiru Ajanah, rasuwa a Abuja bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu ya na da shekaru 64 a duniya.

Marigayi Ajanah, wanda dan asalin karamar hukumar Okehi ne, an haife shi ne a karamar hukumar Okene. Ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamare na Natib Authority da ke Okene daga 1962 zuwa 1968.

Bayan ya kammala makarantar firamare, sai ya zarce kwalejin gwamnatin tarayya da ke Keffi, inda ya kammala a 1973. A 1974, Marigayi Ajanah ya sake komawa kwalejin gwamnatin tarayya da ke Keffin, inda ya samu takardan shaidar babban satifiket na makaranta (HSC) wanda ya kammala a 1975.

Marigayi Nasiru Ajanah ya zarce jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) inda ya samu digirin farko a aikin lauya. Bayan kammala digirinsa na farko ne, sai ya tafi makarantar koyar aikin lauya (Law School) da ke Lagos, inda bayan ya kammala, ya zama cikakken lauya.

Ya fara aikinsa na lauya a ma’aikatan shari’a na Jihar Kwara da ke Ilori, inda ya fara a matsayin lauya jiha, wato ‘State Counsel’. A 1984 ne Alkali Ajanah ya kafa cambarsa mai suna Nasiru Ajanah & Co a garin Okene. Daga bisani a 1989, an nada shi alkali a babban kotun Jihar Kwara, inda a ka maido da shi Jihar Kogi bayan kirkiro ta a 1991.

Kafin nadinsa mukamin Babban Alkalin Alkalan Jihar Kogi, Marigayi Nasiru Ajanah ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban kotun Jihar Kogi, don binciken rikicin Kabba a 1994.

Idan za a iya tunawa dai, mako guda kenan Allah ya yi wa shugaban kotun al’adu ko ‘Customary Court’ na jihar Kogi, Mai Shari’a Ibrahim Shaibu Atadoga, rasuwa bayan ya yi dan fama da gajeruwar jinya.

A lokacin hada wannan labari, wakilin LEADERSHIP A YAU ya samu labari daga majiya mai tushe da ke nuna cewa a na nan a na shiryen-shiryen gudanar da jana’izar Mai Shari’a Ajanah a mahaifarsa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Har ila yau, kawo hada wannan labari, Gwamnatin Jihar Kogi ba ta fitar da sanarwa game da rasuwar marigayin ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: