Daga Abba Ibrahim Wada
Alkalin wasan da ya jagoranci wasan da Ingila ta sha kashi a hannun Argentina a shekarar 1986 dan kasar Tunisia ya ce ya na, “alfahari da girmamawa” da ya taimaka wa Diego Maradona ya ci kwallon da a ke yi wa kirari da ‘Kwallon Karni’.
Maradona, wanda ya mutu ranar Laraba ya na da shekaru 60, ya kacalcala ’ƴan wasan Ingila da dama tun daga tsakiyar fili a kwallo ta biyu da ya ci wa Argentina, minti hudu bayan ya ci kwallon da ta janyo cece-kuce da hannu da a ke kira da ‘Ikon Allah’.
Alkalin wasan, Ali Bin Nasser, wanda yanzu shekarunsa 76 a duniya, ya kuma ce ba shi da zavi illa ya bayar da kwallon farko tare da bayyana cewa, Maradona ya ba shi kyautar riga mai dauke da sa hannunsa lokacin da su ka hadu a shekarar 2015.
“Sun yi kokarin yi ma sa keta sau uku, amma burinsa na samun nasara ya karfafa ma sa gwiwa. Ko da yaushe Ina fadin ‘advantage’ har sai da ya kai ga bakin raga su na kallo sun kasa kayar da shi,” in ji tsohon alkalin wasan.
Ya cigaba da cewa, “Ina kallo daga wajen raga, Ina mamakin yadda wannan dan wasa ya yayyaga mu su tsaron baya tun daga mita 50. Na yi tunanin masu tsaron baya za su yi kokarin kwantar da shi. Ina ta hasashen ko hakan za ta faru kuma a shirye na ke na hura fanariti.”
Ya kara da cewa, “Amma abin mamaki, duk ya yanka mu su tsaron baya da kuma gola (Peter Shilton), ya ci kwallon da a ke kira ‘Kwallon Karni’ kuma Ina alfahari da girmamawa a matsayina na mutum da kuma alkalin wasa, saboda taka rawa a wannan nasarar ta tarihi.
“Idan da na hura keta a yunkuri sau uku da a ka yi, da ba za mu shaida wannan abin mamakin ba. Damar da na bayar ita ce daya daga cikin babbar nasarar da a ke alfahari da ita kuma har yanzu duniya ba za ta manta ba.”
Bin Nasser ya kara da cewa, zagayen dab da kusa da karshe a gasar cin kofin duniya a shekarar 1986, an buga wasan ne gaban ’yan kallo dubu 115,000 a filin Estadio Azteca a birnin Medico, kuma wasan ne kololuwar nasarar aikinsa duk da ya bayar da kwallon farko mai cike da cece-kuce da Maradona ya ci da hannu.
“Dan wasan baya na Ingila [Steve Hodge] ya karvi kwallo, ya mayar da ita baya, amma Maradona ya na sama da Peter Shilton, dukkanninsu ba sa kallo na, sai dai su na kallon mataimakina, wanda dan Bulgeriya ne, Bogdan Dochev.
“Na yi jinkiri da farko, na kalli Dochev, wanda ya koma tsakiyar fili ya na tabbatar da an ci kwallon kuma bai nuna alamar cewa da hannu a ka ci ba. Hakan ya sa ni ma na samu kwarin gwiwar bayar da kwallon.
Dochev, wanda ya mutu a shekarar 2017 ya na da shekaru 80, zai iya cewa, “Fifa ba ta bai wa mataimaka damar tattaunawa da alkalin wasa ba, saboda idan da Fifa ta saka lafazi daga nahiyar Turai a alkalancin wasan, kwallon farko da Maradona ya ci ba za a bayar da ita ba,” in ji shi.
Amma, Bin Nasser ya ce, dattakun da ’yan wasan Ingila su ka nuna abin ‘burgewa’ ne, domin dan wasan gaban Ingila, Gary Lineker, ya tunkare shi ya ce, ‘lafari, ya tava da hannu!’ na amsa cewa: ‘cigaba da wasa!’
“A wajena kwallon ta ciwu dari bisa dari bisa ka’idar Fifa.”
Ya kuma ce, ya so Ingila ta rama, domin a tafi karin lokaci, saboda zafin wasan, amma sakamakon gajiyar da ’yan wasan su ka yi ya sa su ka kasa farkewa.
“Na so a tafi karin minti 30, domin wasan ya kasance mai zafi tun farko har karshe tsakanin manyan kasashe biyu na duniya,” Ali Bin Nasser ya ce, Maradona ya tava kai ma sa ziyara a shekarar 2015.
“Na fada ma sa cewa, ba Argentina ta ci kofin duniya ba, Maradona ne, kuma ya amsa cewa idan da ba da taimakonka ba, da ban ci Kwallon Karni ba, kuma ya ba ni riga da sa hannunsa mai dauke da cewa, ‘Para Ali Mi Amigo Eterna,” in ji Lafarin na Tunisia.