Abba Ibrahim Wada" />

Alkalin Wasa Bai Yi Mana Adalci Ba – Conte

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Inter Antonio Conte, ya caccaki alkalin wasa, bayan doke tawagarsa 2-1 da Barcelona ta yi a ranar Larabar data gabata a gasar cin kofin zakarun turan da suka fafata a filin wasa na Nou Camp.

Bayan dan wasan Inter Laurataro Martinez ya sanya kungiyarsa a gaba da kwallo daya da ya ci a cikin minti na biyu da fara wasan, Suarez ya ci kwallaye biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, wasa ya tashi 2-1.

Amma Conte ya na ganin ba a yimasa adalci ba, don an wa tawagarsa cog eta hanyar nuna son zuciya a wasu hukunce hukuncen da alkalin wasan yayi wanda ya karyarwa da ‘yan wasansa guiwa suka kasa komai.

“Tabbas mun yi wasa mai kyau kuma kowa yasan yadda wasan ya kasance domin munyi kokarin samun nasara a wasan amma saboda son zuciya da kuma kura kurai na alkalin wasa yasa dole said a mukayi rashin nasara” in ji Antonio Conte

Ya ci gaba da cewa “Alkalin wasa ya yi kokari wajen sanyaya wasan duk da cewa wasu daga cikin ‘yan was am sunso su tayar da hankali a wasan saboda haka hakan bazai hana cewa yayi coge ba a wasu hukunce hukuncen”

Conte wanda ya sha kashedi daga alkalin wasa saboda yadda ya yi ta yin mazurai ga alkalin wasan, yana ganin kamata yayi a ba tawagarsa bugun daga  kai sai mai tsaron raga lokacin da aka rafke dan wasan sa Stefano Sensi amma alkalin wasa ya dauke kai.

Exit mobile version