Cibiyar nazarin harkokin jigilar kayayyaki da sayayya da bayar da hidimomi ta hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, alkaluman yawan kayayyakin da masana’antu ke sayarwa (PMI) na kasar a watan Yuni, sun kai kaso 49.7, karuwar maki kaso 0.2 kan na watan da ya gabata.
Duk da cewa akwai sauye-sauye a yanyin tafiyar tattalin arzikin kasar Sin a rabin farko na bana, daga alkaluman na PMI za a iya ganin yadda tattalin arzikin ke ingantuwa da samun tagomashi yadda ya kamata, tare da nuna juriya mai karfi. (Fa’iza Mustapha)