Alkawarin Gyara Nijeriya: Buhari Ba Zai Yarda A Yi Watanda Da Dukiyarta Ba —Lai Muhammad

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa, alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na gyara kasar nan ya sa ba zai taba amince wa a yi watanda da dukiyar al’ummar wannan kasa ba. Saboda haka ya yi tsayuwar daka wajen ganin al’umma sun amfana da dukiyarsu ba wasu tsirari ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani kauye da ake kira Tatabu kusa da Mokwa lokacin da yake duba aikin hanya daga Ilori zuwa Jebba zuwa Mokwa da ke jihar Neja.

Majiyarmu ta shaida mana cewa yanzu haka an kammala gyaran hanyar da nisanta ya kai kilomita 93.6 wanda ya hada da wani yakin hanyar da ta taso daga Ilori zuwa Jebba.

Binciken da majiyar ta mu ta yi ya tabbatar da cewa, wannan hanya da ake gyra babbar hanya ce wadda Kudanci da Arewacin kasar nan da masu kasashen Afirka da ke fito wa daga wadannan bangarori.

Minstan ya ci gaba da cewa, gwamnati na sane da cewa, akwai karancin kudi a hannun jama’a, amma ta gwammace ta yi musu aikin da zai amfani rauwarsu, maimakon ta raba musu kudi su cinye.

Ya ce, wannan gwamnatin ba za ta taba amince wad a irin abin da gwamnatin baya ta yi ban a diban dukiyar al’umma ana watanda da ita ba.

Ya ci gaba da cewa a shekara ukun da gwamnatin APC ta yi ta gyra hanyoyi masu yawa, wadanda suka saukakawa al’ummar kasa wahalhalu wajen tafiye-tafiyensu. Saboda haka sai ministan ya ce, ya kamata al’ummar kasae nan su kara gode wa Allah saboda sauyin gwamnati da suka samu wadda ta damu da al’amarin rayuwarsu.

Exit mobile version