Sabon Dan Madamin Gaya, Dan Majalisar Masarautar Gaya, Alhaji Abdullahi Nayaya ya bayyana nadin da Sarkin Gaya ya yi masa akan wannan matsayin da cewa abin ya dada gode wa Allah ne bisa ni’imar da ya yi masa, tare da godiya ga Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir bisa wannan amincewa da girmamawa da yarda da ya yi masa ya ba shi sarautar.
Ya ce su kuma da aka dora musu wannan nauyi domin su taimaka wa masarautar, suna fata Allah ya ba su damar yin abin da ake tsammani za su yi. Alhaji Abdullahi Nayaya ya ce suna rokon Allah ya ba su damar yin adalci a duk abin da zai zo.
Ya ce a Gina dan’adam da mutum ya san kansa, ya kare mutuncinsa ya kare na makocinsa ya kare mutuncin garinsu da jiharsu da kasarsa da addininsa da jinsinsa, ya san me ya kamata ya yi jama’a su zauna akan adalci da kawo cigaba, bawai a baiwa mutum kudi ba ne.
Ya ce, Sarkin Gaya yana fatan gina jama’a ne, su san kansu da yadda za su gina kasa. Ya ce aikin Danmadami a masarautar Gaya, shi ne yana shiga harka ta addini da kuma yanayin ayyuka da za su taso a kasa, mai martaba zai iya baiwa Danmadami ya kula da shi, ko a yanzu a wannan lokaci akwai harkar wutar lantarki ake da assasa bunkasa harkar ilimi, aikin Danmadami zai iya shiga kowane sashe na ci gaba, in mai martaba ya ba shi umurni.
Shi ma a nasa bangaren, daya daga ‘yan kwamitin nadin na Danmadamin na Gaya, Alhaji Bashir Adamu Gaya ya ce nadin Alhaji Abdullahi Nayaya a matsayin Danmadami kuma Dan majalisar Sarkin Gaya abu ne na farin ciki da masarautar ta yi hangen nesa a kai, da take zabo irin wadannan zakakuran mutane ta ke nadasu. Da ma shi Abdullahi Nayaya Tsohon ma’aikaci ne da ya rike mukamai da dama a Kananan Hukumomi.
Ya ci gaba cewa, saboda haka wannan nadi na Alhaji Abdullahi Nayaya sauyi aka yi masa na sarauta, domin dama yana cikin masu sarauta ta masarautar Gaya.