Connect with us

AL'AJABI

Allah Daya Gari Bamban: Yadda Kabilar Toraja Ke Daraja Gawa Fiye Da Mutum Mai Rai

Published

on

A wannan mako mun kewaya duniya inda muka yada zango a kasar Indonesiya da ke yankin Asiya. A yau filin namu ya yo tattaki na musamman zuwa yankin Gabas-ta-sakiya, inda muka yi nazarin al’adar Kabilar Toraja.

Wani Abu mafi daukar hankali ta yadda har idon duniya ya darsu a kan wadannan al’umma shi ne yanda suke tafiyar da sha’anin gawa ko kuma mu ce mamaci. Su dai wadannan mutane suna rayuwa ne a cikin duwatsun da ke Kudancin Sulawesi ta kasar Indonesia, Kalmar ‘Toraja’ ta samo asali daga yaren “Buginese” ‘Riaja’ wanda yake nufin mutanen kan dutse.

 

Addini 

Akasarin wadannan bayin Allah suna koyi ne da addinin Kiristanci, yayin da wasunsu kuma suka kasance Musulmi, bayan wadannan addinai biyu kuwa wasu daga cikin mutane sun yi imani da addinin bautar dabbobi, wanda aka fi sani da “Aluk” (hanya). Wani abin al’ajabi kuwa shi ne, mutanen sun yi imani cewa, Ubangizansu sun sauko ne daga sama, da taimakon tsani, a cewarsu. A wannan lokacin shi ne hanya mafi kusanci ko kuma sauki wajen sadarwa tsakanin al’ummarsu ta Toraja da kuma Ubangizansu.

 

Auratayya

Mutanen Toraja suna auren mace daya, duk da kasancewar a wani zamani da ya shude masu sarauta ko mulki suna da damar auren mace fiye da daya. Ita ma macen tana da damar auren namiji fiye da daya. Sukan yi aure na hada ka, ma’ana hadin iyaye ko wasu manya, sannan namiji yana da damar ya ga mace ya ce, yana so. Wato ma’ana sukan yi kuma auren zabi. Ba su amince da auratayya tsakanin ’yan’uwa na kusanci ba, sai dai na nesa. Amma a wani zamani can baya sukan yi auratayya tsakanin ’yan’uwa mafi kusa, ta hanyar sadaukar da jinin dabbobi. Sun yarda da saki a cikin aure kuma wanda ya yi saki ko wacce aka saka za ta iya yin sake aure.

 

Allah daya gari banban

Wani abin ban mamaki dangane da wannan al’umma shi ne yadda suke tafiyar da mamaci. Su dai wadannan al’umma babu abin da suka fi karramawa kamar gawa. Sukan daukaka mamaci fiye ma da wanda yake raye. Idan mutum ya mutu akan share sati, wata ko ma shekara ba tare da an bisne shi ba. Duk tsawon lokacin mamaci zai dauke su tare da iyalansa kamar lokacinda yake raye. Hikimar yin haka, shi ne, domin su sami wadataccen lokacin da za su tara abin da za su yi bikin bisne mamacin da shi. Sukan yi amfani da wani sinadari nasu da zai hana mamacin rubewa ta hanyar zubawa mamacin.

Biki ne ake yin sa gagarumi na gani na fada wanda ke samun halartar ’yan’uwa, abokan arziki, da kuma iyalan mamacin. Sukan dauki tsawon kwanaki ko satattaki domin gudanar da wannan biki da suke kira “Rambu salong” ya yi gudanar da bikin za a yanka manya-manya bijimai da aladu. Bayan an yayyaanka sai a sarrafa naman sannan a rarraba wa mutanen da suka halarci bikin bisa la’akari da matsayinsu.

Rana ta goma sha daya da wannan biki ita ce ranar da ta yi daidai da lokacin da za a binne mamacin. Za a tona cikin duwatsa a bisne gawar, sannan sai a yi amfani da kaho irin na dabbobin da aka yanka wajen bikin, wajen kawatar da kabarin, yayin da wasu kuma daga cikin ake jerewa domin kwalliya a kofar gidansu mamacin. Yawan kahonin da aka yi amfani da su domin kawata gurin shi ke tantance iya matsayi ko girman mamacin.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba, daya daga cikin al’adarsu ita ce tono mamaci daga inda aka bisne shi bayan kowacce shekara ]aya, yayinda duk shekara ta zagayo za a tono gawar sai a dawo a sake wani gagarumin bikin. Yayin da aka sheka wa mamacin kwalliya ta musamman, daga bisani a mai da shi makwancinsa a rufe,

Daga cikin wadannan kabilar kuma akwai wadanda su sam ba sa bisne gawa, a madadin haka kuwa, sai a tabbatar an zuba masa wannan sinadari ta yanda ba zai baci ba. Kana a sanya shi cikin wani daki da aka tanadar dominsa bayan an yi masa kwalliya ta kece raini. Yayin da lokaci bayan lokaci akan bude dakin a ciro mamacin sannan a sake yi masa kwalliya a maidashi, Ikon Allah ikon gaske!

Haka dai rayuwar wannan kabila ta Toraja ke kasancewa a duniyar nan. A yayin da wasu ke ganin da zarar ran mutum ya fita daga jikinsa gawarsa ba ta da wani amfani illa a yi sauri a binne ta, su kuwa gawar ita ce mafi alfanu a wurinsu bisa la’akari da irin gatan da suke mata. Wannan shi ne, Allah Daya Gari Bamban.

 
Advertisement

labarai