Allah Ne Ya Umarce Ni Na Tallafa Wa Marasa Galihu – Ekene Adams

Daga Abubakar Abba,

Wani tsohon dan kwallon kafa kuma tsohon dan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya a karkashin inuwar jamiyyarsa ta APGA zaben 2019 daga mazabar Chikun da Kajuru Mista Ekene Adams ya sanar da cewa, Allah ne ya nufe shi ya tallafa wa marasa karfi da kuma wasu tsofaffin yan kwallon kafa a jihar.

Mista Ekene ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da sabon ofishin tallafa wa marasa karfi a Sabon Tasha da ke a Kaduna.

Ya sanar da cewa, ya yi hakan ne domin su samu sana’oin da za su iya zamowa masu dogaro da kawunansu, inda ya ci gaba da cewa, a kashi na farko na shirin, ya rabar da naira miliyan 4.5 ga wadanda suka amfana su 45.

Mista Ekene ya ci gaba da cewa, mutane su 220 da suka fito daga kananan hukmoim Chikun da Kajuru kuma wadanda suke yin sana’oi a zahiri kuma suke bukatar tallafin kudade, sun amfana da naira miliyan 12.

Ya yi nuni da cewa, mun san cewa, cutar Korona ta shafi rayuwar jama’a ta yau da kullum, musamman marasa galihu a a daon hakan, ya zama wajibi a bayar da tallafin domin a rage masu radadin da ta jefa su a ciki.

A cewarsa, a saboda haka ne naga ya dace in bayar da wannan tallafin ta hanyar yin afmanbi da ‘yar dukiyar da Allah ya bani

Mista Ekene ya sanar da cewa, ba wai ya bayar da tallafin bane domin wata manufa ta siyasa ba, amma Allah ne ya umarce ni ya kuma bani ikon bayar da tallafin.

A nasa jawabin a gurin taron, mai bai wa gwamna n jihar shawara kan harkokin siyasa Mista Ben Kure ya yaba wa Mista Ekene kan wannan kokarin, inda ya yi nuni da cewa, tallafin zai taimaka wa wadanda suka amfana matuka.

Mista Ben Kure ya sanar da cewa, gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai za ta yi dukkan mai yuwu wa wajen samar da kyakawan yanayin yin kasuwanci a jihar.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin Mista Bola Bello da kuma Mista Joshua Daniel sun yaba wa Mista Ekene kan tallafin.

Kayan da aka rabar sun hada da, Injinan nika, baburan hawa kudade da sauransu.

 

Exit mobile version