Allah Ya Ganar Da Talakawan Arewacin Nijeriya

Daga Ado Umar Lalu

A makon da ya wuce na ji wani labari mai ban takaici wanda wani Babban Malamin Jami’a ya sami wani babban ɗan siyasa inda ya ja hankalin da tare da roƙonsa a kan ya yi wani yunƙuri domin ya taimakawa matasan da ke kewaye da shi su koma makaranta.

Babban abin ban haushi da takaicin da ya fito daga bakin wannan bawan Allah shi ne “idan suka koma makaranta to su wa za su yi mana harkar siyasar? Gwara su zo kullum na basu dubu ko dubu da dari biyar”.

Wannan karara ya fito da irin halayyar mafi yawancin yan siyasar mu a fili na yadda ƙaunar talakansu dai bata wuce ta baki ba.

Da yadda suke faɗa suna kaunar talaka da gaske suke to tabbas da basu fifita Yayan su, Yan-Uwa, Abokai da Dangin Matayen su ba akan talakawan da su suka zabe su.

Ba zaka taba ganin ‘ya’yan ‘yan siyasa, wurin kamfen ba, ko ka ga suna ‘agent’ ballantana murna idan iyayen nasu sun kai ga nasara ba sai wajen bada shaidar cin zabe nan ne za mu ga mata da ‘ya’ya an dau wanka wajen rakiya amma waɗanda suka yi wahala an shafe su.

Bayan rantsuwa babu abin da suka fi mayar da hankalin su akai fiye da gina rukunin mutanen da na lissafa a sama wajen basu ingantaccen ilimi a ciki da wajen Nijeriya, basu aiki a manyan ma’aikatun da suka zama haramiyar talakawa, harkar kwangila sun mata babba da jaka sai kamfanonin su da wayanda suke so. Amma da zabe ya zo kaga fosta tana yawo da murmushin karya na yaudara an lallabo sake yi wa talakawa wayo da dadin baki.

A yau dai a Arewacin Nijeriya tun bayan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto babu wani ɗan siyasa da ya taimaki talakawa wajen samun ilimi a matakai daban daban kamar Tsohon Gwamna Kano Mai-Girma Sanata Rabi’u Kwankwaso ba wanda ya zama gatan marar gata wajen harkar ilimi.

Duk da cewa wadansu masu gajeren tunani suna ganin siyasa ce, to amma sun manta shi Sanata Kwankwaso siyasar ta kai shi da kuri’un talakawa kuma yayi amfani da ita domin ya amfanar da jama’ar sa, mai ya hana ku fadawa iyayen gidan naku suma suyi irin wannan siyasar da za a wayi gari a garuruwan su za su nunawa duniya a yau suma sun kyankyashe masu manyan digiri da digirin digirgir.

Duk wanda ya taimaka maka wajen harkar ilimi musamman daukar nauyin ka domin kaima a wayi gari ka zama wani a rayuwa mai dogaro da kan sa har ya taimaki wasu.

Babu abin da ke canza rayuwar mutum irin ilimi, ya sa ya fahimci rayuwa, ya rabe tsakanin gaskiya da yaudara da kuma rabuwa da makauniyar soyayya ko adawa.

Dole ne mu kara hangen nesa mu gane cewar mudai talakawa Yansiya kadan ne ke son mu romon baka yafi waya. Lokacin da ake fafuta kune a gaba amma da an kai ga nasara kun zama abun kyama sai dai marassa zuciya ne za su rika kai komo a cikin su. In dai kasan ciwon kan ka to kayi nesa dasu domin kana tunkarar su za su turbine fuska ko murmushin karya amma basa son a kusance su.

Nan ba da jimawa ba za ku ji sunan wannan mutumin da yardar Allah.

Ado Umar Lalu

 

 

Exit mobile version