Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Allah Ya Toni Asirin Duk Mai Hannu A Ta’addancin Katsina – Addu’ar Sakataren Gwamnatin Jihar

by Muhammad
January 11, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Ta'addancin
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Sagir Abubukar,

Shugaban kwamitin tsaro na jihar Katsina kuma Sakataren Gwamnati Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya roki al’umma da su dukufa yin addu’o’in samun dawammamen zaman lafiya, da kuma addu’ar Allah ya toni asirin duk wanda ke da hannu a cikin sace-sacen mutane da kashe-kashen yan bindigar ke yi a jihar Katsina dama Nijeriya baki daya.

samndaads

Malam Mustapha Muhammad Inuwa, ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabin bankwana ga wasu mutane talatin da bakwai da gwamnatin jihar Katsina ta kubutar a hannun yan bindiga, a sasanin ‘yan yi wa kasa hidima da ke kan hanyar Mani a cikin garin Katsina.

Dakta Mustapha Inuwa ya kara da cewa masu aikata wannan ta’addanci, akwai masu taimaka masu cikin mutanen gari, sai mu yi ta fatan Allah ubangiji ya yi mana maganin su ya kuma kawo karshen sa. Duk wanda ke da hannu a cikin wannan ta’addanci ko ta kowacce hanya, Allah ubangiji ya yi mana maganin su. Wadanda ke kokarin kullum su ga an samu zaman lafiya kamar su jami’an tsaro da masu rike da madafun gwamnati da mutanen ke addu’a a samu zaman lafiya, Allah ya ci gaba da ba mu nasara kawo karshensa a jihar Katsina da ma sauran jihohin kasar nan da ke fama da makamanciyar wannan matsalar.

Daga karshe, ya ce gwamnati jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, za ta ci gaba da yin bakin kokarin ta, na ganin tsaro ya inganta a jihar Katsina. Samar da tsaron lafiya da dukiyoyin su, hakki ne da ya rataya a wuyanmu, amma al’umma sai sun ci gaba da ba da hadin-kai, kamar yadda suka saba. Kuma gwamnan jihar, Alhaji Aminu Bello Masari, ya ba su dan hassahi na kudi da za su tafi.

Gwamnatin Jihar Katsina, cikin satin nan ta kubutar da mutane dari da arba’in, wadanda aka kubutar da su a hannun ‘yan bindiga, ta hanyar yin sulhu ba tare da sun biya kudin fansar ba. Masari ya bayyana cewa damar da muka samu ta amso daliban makarantar sakandire ta Kankara, su dari ukku da arba’in da hudu, ita ce mu ke amfani da ita, don mu ga duk wanda ke tsare hannun yan bindigar nan, mun kubutar da shi, ba ma dan jihar Katsina ba kawai, dama ce da aka samu don kar ta kucce.

SendShareTweetShare
Previous Post

Minista Sadiya Farouk Na So A Kula Da Nakasassun Nijeriya Kamar A Kasar Waje

Next Post

Shugaban INEC Ya Yi Kira Ga Majalisar Tarayya Kan Kwaskwarimar Dokar Zabe

RelatedPosts

’Yan Sandan Italiya

’Yan Sandan Italiya Sun Kama ’Yan Nijeriya 16 Masu Sana’ar Miyagun Kwayoyi

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Rahotanni daga Kasar Italiya sun zo da ingacin cewa a...

miyagun kwayoyi

NDLEA Sun Cafke Mutum Uku Da Hodar Iblis A Legas

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA),...

’Yan Fashi

’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan Dan Uwan Akanta Janar Na ​​Imo

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

’Yan sanda sun tabbatar da kisan dan uwan ​Akanta Janar...

Next Post
INEC

Shugaban INEC Ya Yi Kira Ga Majalisar Tarayya Kan Kwaskwarimar Dokar Zabe

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version