Allah Ya Yi Wa Mahmoon Baba-Ahmad Rasuwa

A Daren Alhamis din nan ne Allah ya karbi ran shahararen dan jaridar na Mahmoon Baba-Ahmed  samakon gajeriyar rashin lafiya da ya yi. Marigayin ya rasu yana da shekara 74 a duniya. Ya fara aiki a gidan rediyon CBNN a sheakara ta 1971, daga nan ya zama wakilin da ke aiko wa gidan rediyon labarai a jihar Bauci da Kano da da Fulato, A shekara ta 1983 gwamnatin jihar Kano ta ba shi mutsayin shugaban gidan rediyon jihar Kano. Har zuwa karshen rayuwarsa ya na bayar da gudummawa a jaridar Aminiya da Bluueprint. Tuni dai aka yi jana’izarsa kmar yadda adninin Musulinci ya tana da.

‘yan jarida da dama sun nuna alhininsu bisa wannan rasuwa, kuma sun nuna cewa, lallai rasuwarsa babban gibi ne a harkar aikin jarida a kasar nan, wanda kuma cike shi zai yi wuya.

Majiyarmu ta shaida mana cewar daga cikin wadanda suka halarci jana’izar marigayin sun hada da gwamnan Borno Gob. Kashim Shettima, mataimakinsa Usman Durkwa, da kuma mambobin majalisar dokokin Jihar.

Exit mobile version