Khalid Idris Doya" />

Allah Ya Yi Wa Sanatan Bauchi Ta Kudu Ali Wakili Rasuwa

Daga Khalid Idris Doya

Da safiyar jiya Asabar ne Allah mai yadda Ya so ya amshi ran Malam Ali Wakili, wanda shi ne sanatan Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya. Malam Ali Wakili ya rasu ne ya na da shekaru 58 a duniya, 58.

Makusantan marigayin sun shaida cewar, rasuwar tasa ta na zuwa ne a sakamakon wata ’yar gajeruwar rashin lafiya da ta same shi a gidansa da ke Gwarimpa a birnin tarayya Abuja, inda a ka garzaya da shi asibiti, domin samar ma sa da lafiya, to amma a can asibiti ne wa’adin rayuwarsa ya cika, inda ya ce ga garinku na.

Rahotanni su nuna cewar, Ali Wakili ya halarci daurin auren diyar hamshakin mai kudin nan, wato Aliko Dangote a jihar Kano, auren da a ka daura a ranar Juma’a, wato kwana guda kafin rasuwarsa.

Wani makusancin marigayin, Malam Musa Azare, ya shaida wa wakilimu ta wayar tarho cewar, dan halartar wani daurin aure a jihar Adamawa a garin Yola, inda har ya umurci dirabansa da ya dauke shi zuwa tashar jirgin sama, amma ashe kwana ya zo karshe.

An yi wa Malam Ali Wakili sutura hade da kai shi makwancinsa na dindidin ne da misalin karfe 1:30 na ranar jiya Asabar, 17 Maris, 2018, bayan an yi ma sa sallah kamar yadda addinin Islama ta shimfida a babban masallacin kasa da ke Abuja.

An binne Sanata Wakili ne a makabartar Apo da ke birnin tarayya Abuja, wato unguwar da gidajen ’yan majalisar tarayya ta ke.

A wajen jana’izarsa, tuturuwar shuwagabani, ’yan majalisa, gwamnoni ciki har da gwamnan jiharsa, M. A Abubakar, kakakin majalisar dokokin Nijeriya Yakubu Dogara da sauran ’yan Nijeriya ne su ka jagoranci yi ma sa jana’iza tare da yi ma sa rakiya zuwa kabarinsa a makabarta.

A sakonsa na ta’aziyya, gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya nuna alhininsa da rashin mamacin, sannan sai ya yi fatan Allah ya gafarta wa Ali Wakili ya kuma sanya rahamarsa a gare shi.

GMA ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga ’yan uwa da abokan arziki, gami da illahirin jama’ar jihar Bauchi, musamman mazabar Bauchi ta Kudu, bisa wannan babban rashin.

Ta bakin gwamnan Bauchi, “a madadin gwamnan jihar Bauchi da ita kanta gwamnatin ta Bauchi mu na addu’a Allah ya ji kan wannan da namu na Bauchi, Ya Rahamshe shi, Ya kuma sa aljanna ta zama makomarsa. Mu na kuma addu’ar Allah Ya baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi,” in ji gwamnan ta bakin Shamsuddeen Lukman, mai tallafa ma sa kan kafafen sadarwa.

Haka zalika, ita ma matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar, ta fitar da sakon jajenta jim kadan bayan rasuwar, inda ta yi addu’ar Allah ya gafarta wa Ali Wakili ya sanya makomarsa ta kasance Aljannace.

LEADERSHIP A YAU LAHADI ta labarto cewar, tuni dai al’ummar jihar Bauchi su ka yi ta nuna alhinunsu kan wannan rashin da kuma yi ma sa addu’ar Allah ya ji kan shi.

Wakilimu ya labarto cewar Marigayin Sanata Ali Wakili ya rasu ya na da shekaru 58 a duniya, ya bar mata biyu da kuma ‘ya’ya 11 a duniya.

Gabanin rasuwarsa shi ne shugaban kwamitin shawo kan talauci na majalisar dattawan kasa, kuma ya samu kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu ne a zaben da a ka fafata na 2015 a karkashin jam’iyyar APC.

A sakon ta’aziyyar da jam’iyyar APC na jihar Bauchi ta fitar, wanda sakataren tsare-tsare na jam’iyyar a matakin jihar Bauchi ya sanya wa hannu, ta nuna matukar jimaminta da rashin kan rashin daya daga cikin mambobinta.

“A madadin jam’iyyar APC ta jihar Bauchi mu na mika sakon ta’aziyyarmu ga gwamnatin jihar Bauchi, iyalan marigayin, masarautar Bauchi da kuma illahirin jama’an jihar a bisa rasuwar danmu, Sanata Malam Ali Wakili mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu a majalisar dattijai. Allah ya yi ma sa rahama ya sanya aljanna ta kasance ma sa gida. Mun ji zafin rashin nan,” a cewar Gyengyen.

 

Exit mobile version