Abba Ibrahim Wada" />

Allison Becker Ya Dawo Da Karfinsa – Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce mai tsaron ragar kungiyar Alisson Becker na gab da murmurewa daga raunin da ya samu, inda ake sa ran ya buga wasa a wasansu da Leceister City ranar Asabar gabanin wasansu da Manchester United.

Alisson mai shekaru 26 wanda yanzu haka shi ne mai tsaron raga mafi kwarewa yanzu a duniyar kwallo, ya rasa wasannin Liverpool har guda tara tun bayan samun rauni a wasansu na farko da suka kara da kungiyar Norwich City ranar 9 ga watan Agusta.

A jiya Laraba ne, Liverpool ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Red Bull Salzburg a gasar zakarun Turai, gasar da za a iya cewa ta zowa kungiyar a bai-bai duk da kasancewarta mai rike da kambunta.

A cewar Klopp Liverpool yanzu haka gwarzon mai tsaron ragar ya fara halartar filin atisaye a ranar Talata, kuma suna sa ran bangaren masu kula da lafiya na kungiyar zasu bashi izinin fara buga wasa.

Bayan wasan Liverpool da Leceister City da kuma gajeran hutun da kungiyoyin kwallon kafar za su fara, a ranar 20 ga watan Octoba ne za ta kara da Manchester United karkashin gasar firimiyar kasar Ingila.

Sai dai kociyan dan kasar Jamus ya bayyana cewa yana fatan ganin Becker ya dawo da karfinsa kuma ya fara wakiltar kungiyar a fafatawarsu da Manchester United wadda kawo yanzu take cikin matsalar rashin samun nasara a wasanni.

Exit mobile version