Connect with us

LABARAI

Almajirai Suna Da ‘Yanci Kamar Kowane Dan Nijeriya A Tsarin Mulkin Kasa – Goni Zangina

Published

on

  • Barayin Gwamnati Suka Jefa Su Cikin Halin Bara

Daya daga cikin Malaman da ke koyar da Alkur’ani mai girma, Goni Zangina da ke Jihar Neja ya bayyana cewa Almajirai suna da ‘yanci kamar kowane Dan Nijeriya a bisa tsarin mulkin kasar nan, don haka Gwamnonin Arewa su sake shawara dangane da yadda suka tafiyar da sha’aninsu a kasar nan.
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da LEADERSHIP A Yau Juma’a, a jiya Alhamis.
Ya fara da bayyana cewa, “Kungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya ku saketsari a bisa irin gallazawa da tozartawa da kuke yi a kan ‘yan’uwanmu masu karatun Alkur’ani wato Almajarai masu karatun allo. Hakika wannan abin takaici ne kwarai idan aka yi la’akari da cewa su ma ‘yan kasa ne, kuma suna da hakki kamar kowanne dan kasa na zaba wa kansa irin ilimin da yake bukata ya yi da addinin da yake bukata ya yi kamar yadda ya zo a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
“Na yi mamaki matuka yadda wusu daga cikin masu fada-a-ji a cikin wannan gwamnati suke danganta Almajirai da ta addanci alhali wannan karya ce da kazafi da kage, sanin kowa ne babu dan ta adda irin mutumin da aka dauki amanar mutane ta hanyar ba shi mukami na gwamnati ta hanyar tsaro, ko ilimi ko lafiya ko tattalin arziki da sauran amanonin al’umma, amma ya mai da su dukiyarsa, wanda wannan ne ya sa masu bara yin bara, ya sanya barayi yin sata, ya haifar da ta’addanci iri-iri a Nijeriya.
“Ko ba komai da wadanda aka ba su rikon amana sun yi abin da ya dace sun mai da amana ga ma abota ita, da ba a samu masu bara ba, da an yi wa karatun alkurani tsari a gwamnatance kamar yadda sauran kasashen duniya da dama suka yi, da ba a samu masu bara ba.
“Gwamnonin Arewa ku sani cewa wadanda kuke kamawa kuke wulakantawa tare da tozartawa suna da hakki a kanku, kuma Allah zai tambaye ku a kan hakkinsu a kanku ka da ku manta da irin gudunmawar da Malamn tsangaya suke baku musamman lokutan zabubbuka ta hanyar ba ku kuri’a da addu’o’in da suke muku har kuka samu nasara, kar ku manta da irin gudunmawar da Malaman alkur’ani suke ba wa Nijeriya ta hanyar addu’ar zaman lafiya da ci gaban kasa kar ku manta lokacin yakin basasar kasar da irin gudun mawar da Malaman alkur’ani suka bayar, wannan shi ne sakamakonsu a wurinku?
“Ba ku basu hakkinsu na ‘yan kasa ba, sannan baku bar su sun zauna lafiya ba, mai ya sa ba za ku taimaki wannan hanyar ta fuskar gyare-gyare domin ya dace da karatun zamani. Mai ya sa kuke tunanin za ku iya kau da wannan hanyar cikin sauki, mai ya sa ba za ku nemi shawarar masana a kan wannan hanyar ba?”
Ya yi kiran a sake shawara kan yadda ake tafiyar da sha’anin Almajiran, yana mai cewa, “To lallai ku canza tunani, domin wallahi ba za ku iya kau da wannan hanyar ba, Allah ba zai baku sa’a ba, domin hanyar a ke bi wajen haddace littafinsa ce aka rubutawa a cikin wannan hanyar a ke samar da kowanne irin gogaggen mahaddaci a ke samar da kowanna irin gogaggen marubucin alkur’ani mai tsarki.
“A karshe ina kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dubi wannan al’amarin da idon basira domin kawo masana da za su inganta hanyar karatun tsangaya kamar yadda gwamnatin da ya gada ta fara yi. Muna addu’ar Allah ya zaunar da kasarmu lafiya, Allah ya yaye mana wannan annoba ta Korona da sauran abubuwan da suka damu kasar nan amin,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: