A ranar Juma’a ne wanda ya yi daidai da 1/1/2021 almajiran Shiek Ibrahim Yakuk El-Zakzaky na garin Samaru da kewaye a karamar hukumar Sabon Garin Zariya suka kai ziyara cocin cccc don tayasu murnar shiga sabuwar shekarar 2021.
Tawagar ta Almajiran bubban malamin da akafi sani da mabiya darikar Shi’ar sun ciyarci cocin ECWA ne dake anguwar Bido a karamar hukumar Sabon Gari mazansu da matansu cikin tsari da natsuwa.
Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labari da suka shaida yadda ciyarar ta gudana a ranar.
Bayan tarba ta musamman da ma ziyarar suka samu daga bangaren mabiya addinin kisatancin a cikin cocin, bubban limamin cocin ya bayar da dama ta musamman don rera ma bakin wakoki dake alamta godiya da maraba.
Malam Ibrahim Isa daga jami’ar Ahmadu Bello Zariya na daya daga cikin tawagar kuma shi ya gabatar da Malam Murtala Bomo da nufin bayyana dalilan kawo ziyarar kamar haka.
Malam Murtala Bomo ya baiyyana kulla zumunci da fahimtar juna ne makasudin zuwansu wannan ziyara kamar yadda shugabansu Shiek Ibrahim El-Zakzaky ya koyar dasu.
Kuma malamin ya kara da cewa mabiya Shiek Ibrahim El-Zakzaki a duk ranar kirsimeti da ranar sabuwar shekara sukan ziyarci mabiya addinin kirista don taya juna murda bisa koyarwar da tarbiya da suka samu wajan malamansu mabiya iyalan gidan Annabi Muhammad Allah ya kara masa aminci .
Bayan cin dalilin ziyarar tasune sai aka basu dama ta musamman da har suka gayyaci wani mawaki daga cikin tawagar tasu mai suna Mujahid Awwal Nasir ya rerawa Annabi Isa (as) waka dake nuna murna da zuwansa Duniya.