Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Almajirancin Kananan Yara: Ina Mafita?

by
4 months ago
in TASKIRA
6 min read
Almajirancin Kananan Yara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Rabi’at sidi Bala,

Tsokacin mu na yau ya yi duba ne game da yadda kananan yara almajirai ke yawo a gari tamkar ba su da mahaifa, duk da cewa wasu yaran da ake turo su almajiranci marayu ne ba su da iyaye, amma wasu da iyayen ana turo su ne domin samun abun duniya ta bangaren iyayensu kenan. Yayin da wasu kuma ake turo su domin daukar darasi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, yin hakan a yanzu babbar matsala ce ga tarbiyyar yaran, domin kuwa dabi’unsu na sauyawa zuwa wasu dabi’un na daban kamar shaye-shaye, dabanci, sace-sace, fashi, da dai sauransu. A yanzu almajirai na yawaita fiye da misali tarbiyyarsu kuma na gurbata, maimakon a sami karatun da ake bukata, sai a sami akasin haka. Ko tawacce hanya za a bi domin magance wannan matsalar? Wanne kira za a yi ga su iyayen da suke tura yaransu almajiranci? Ko mene ne amfanin ko rashin amfanin tura yara kanana almajiranci? Wannan shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa inda suka fayyace nasu ra’ayoyin game da wannan lamari, ga dai bayanan nasu kamar haka:

Aisha Musa ‘Yankara:

Labarai Masu Nasaba

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

A nawa mahangar abinda ke jawo yawan almajirai shi ne rashin bawa yara kulawar da ya kamata ga iyaye ko da anga yaro ya dan fara yin wani abu wanda bai kamata ba sai a daukeshi a kaishi makarantar Allo, alhalin wallahi wannan babbar barazana ce ga rayuwarnnan na sani iyayenmu kakan ninmu sun yi hakan amma a lokacin duniyar ba ta lalace haka ba, amma yanzu fa akwai almajirin da za ki gani wallahi ko wanka ba ya iyawa kanshi, amma mahaifiyarsa da mahaifisa, su daukeshi su kai almajiranci a bugi yaro a can a muzguna mashi a can a wulakanta shi a can ya rasa wurin kwana ya rasa abincinsa ka ma bakin sa, ta yau ya yaro ba zai canja hali ba ya bi wata turbar ta daban? A matsayinki na uwa ko a matsayinka na uba Idan yaro ya fara nuna wani hali wanda bai kamata ba, ba almajiranci ya kamata a kaishi ba jawoshi za a yi a jiki har a gane menene matsalarsa to a gabanku ya lalace fi sabilillahi ta ya zai shiryu a gaban wasu, idan ba Allah ya shiryar da shi ba wallahi duk inda kika kai da son ganin yaronki ya zama na kwarai matukar ubangiji bai kaddara hakan ba babu wanda ya isa ya shirya maki yaro. Ta hanyar kulawa ga yaran domin kuwa diya kiwo ne da ubangiji ya bawa iyaye, za a magance hakan ta hanyar gyara makarantun ya zamana ko da za a kai yaro makaranta to za a hada shi da komai da zai bukata, haka lokaci bayan lokaci a matsayinku na iyaye ku rika zuwa kuna gaishe shi, ba wai ku yi banza da yaro ba abinda iyayenmu da kakanninmu suke yi sai ace idan aka kai yaro makaranta ba zai dawo gida ba ba zai ga kowa na sa ba har sai ranar da ya dauke alkurani fisabilillahi Idan da ana yin hakan yanzu ai hakan ba mai yiwuwa bane a ko wane gari kuke akwai makarantar allo ba dole bane sai an kai yaro wani gari ya je ya yi ta gararamba, a saka shi ta cikin gari ya je ya dawo ki wanke abinki ki bashi abinci ya yi wasa cikin abokanshi wadanda kika san su shi ma ya sansu amma kun kai yaro wani gari dan Allah taya ba zai hadu da abokan banza ba to ai wasu iyayen ba su dauki diyan da muhimmanci ba ki ji uwa tana kiran danta shege ko dan iska hana baiwar Allah haba! ba ki gyara danki ba shi ne wani zai gyara maki? yau kwana biyu na wuto wajen ‘stadium’ akwai wasu almajirai a wajen kin san Allah yaron ko wanka bai iyawa da robar shi a hannu duk wannan uban sanyin yaron babu kayan arziki a jikinsa sai takurewa yake jiki duk ya bushe ke uwa kina can kina bacci ai yaro yana makaranta, Akwai uwar da take cewa yaron idan zai dawo ya siyo kaya ka za da Ka za, fi sabilillahi idan ba ya sana’a kika ce mi shi hakan me ake tunanin zai faru?.

Abdul’azeez Shehu (Yareema Shaheed) 08030704570 daga Jihar Kano:


To dalilin da ke sa wasu iyayen sakin yaransu wasarere shi ne; wasu iyayen ba su da ilimin zamantakewar iyali shi ya sa suke yin haka ba tare da sun yi tunanin abin da zai faru ba. Kira na ga iyayen yara su ji tsoron Allah, idan za su turo yaransu Almajiranci to su tabbata sun siya masu kayan abinci da sutura kuma su ba malamin kudin magani ko da rashin lafiya ya kamasu. Amfanin tura yara Almajiranci shi ne za su taso da madarar ilimi kuma su ne za su za ma malamanmu nan gaba. Amma dole sai iyaye sun daukin nauyin cin su da shan su, bawai su barwa Malami ragamar komai ba. Hanyar da za a bi don gyara wannan matsalar su ne, Gwamnati ta fitarwa da makarantun Allo tsarin da ya da ce domin hakan shi zai sa duk wannan matsalolin su kau.

Lubabatu Auta Ingawa:


Iyaye kun san da cewa a halin da ake ciki yanzu babu tsangayar da babu makaranta idan babu kusa da kauyenku akwai a gari mafi kusa daku, mai zai hana ku saka ‘Ya’yanku makarantun Boko, Islamiyya da kuma ta Allon duk a in da kuke, hakan zai sa kusan shiga da fitar ‘ya’yanku, ku san cin su da kuma shan su, tura ‘ya’yanku Almajiranci ba tare da abinci ba, ba tare da bibiyar halin da suke ciki ba ganganci ne, ‘ya’yanku suna shiga cikin mayuwacin hali ya yin da suka nemi abinci suka rasa, rashin abinci yana hana su samun nutsuwar karatun da kuka turo su domin shi, iyaye ina baku shawara idan har ya zama lallai sai kun kai ‘ya’yanku makarantar Allo to ku dinga hadasu da abincin da za su ci da ziyartarsu a kai- a kai kamar yadda ake ziyartar daliban makarantar kwana (Boarding school).

Princess Fatima Zahra Mazadu daga Gombe:


Abu na farko Neman ilimi, yunwa da talauci, kiriniya, rashin ji. Abu na biyu yawaita ziyartar yaro akan lokaci, taimakon malaman da abun amfani, shi zai sa danka ya samu kulawa, ta musamman. Na uku Amfanin shi ilmantuwa, natsuwa, da koyan zaman duniya, in har yana samun kulawa. Rashin amfaninsa, lalacewa da shiga wasu harkoki da abokan banza, musamman in ba a zuwa duba shi daga gida, Malamai wasu ba su da lokacin gyara, in har iyayen na banzatar da yaro, dan daga sun fara girma, suna barin hannun gardawa ne. Abu na hudu roko zuwa ga gomnati wurin taimaka musu, masu hali suke yawan basu sadaka, killacesu yawon barace-bara ce duba ga kankantar su, Almajirai lamarinsu sai Allah. Tabbas!Almajiranci abu ne na halak! dan neman ilimi kuma wajibi ne amma yanzu an maidashi na tura yaro in ya dameka a gida ko na neman abunda za a ci.

Ummee Yusuf daga Maiduguri:


Wasu rashin wadata ne wasu kuma maraici, sannan na wasu kuma sakaci ne daga wajan iyayen. Ya kamata su san cewa yara amana ne a wajan mu wanda Allah ya bamu dole ne mu kula da duk wani nauyin su da Allah ya daura mana. Rashin amfanin ta ya fi amfaninta yawa domin yawancin yara maimakon su samu ilimin addini kamar yadda ake fata sai dai su lalace su zama barayi, ko kuma ‘yan ta’adda. Hanyan da nake ganin za a gyara cikin sauki shi ne gommanati ta sanya ido kan malaman ko ya zama wajibi su kula da cin su da shan su domin yawancin su yunwa ce ke saka su fadawa mugayen hanyoyi.
Jingina ga ‘yan ‘golden pen writers’ ina gaishe su.

Fatima Usman Umar Kano Layin Pol R/lemo:


Ya kamata iyaye su rinka kulawa da tarbiyyar ‘ya’yansu saboda rayuwar ‘ya’yansu ta kasance mai amfani anan gaba, al’umma sun yi alfahari da su da irin tarbiyyar da su ka samu. Anan dai kirana ga iyaye su sani cewa ba sai sun tura ‘ya’yansu almajiranci ne za su samu ilimin addini ba. A gaban su ma su iya samun ilimi da tarbiyyar. A halin yanzu rayuwar da muke ciki malaman tsangaya basa samun damar yin tarbiyyar ‘ya’yan da ake kawo musu. Amfanin turawar shi ne domin su samo wayewa da rayuwa irin ta zamani tare da ilimin Islama, Rashin amfaninsa kuwa shi ne, Yaran ba sa samun kulawa da tarbiyya da kuma soyayya ta iyaye da dai sauran su. Hanya daya ce dukkan al’umma su tashi tsaye wajen kawo can ji a almajiranci ta hanyar kulawa da yaran da ake kawowa karatu. Gwamnati kuma ta yi tsari bawai hana bara ba.

Khadijarh Muhd Sha’aban daga garin Kano:


A gaskiya wannan abun yana ci min tuwo a kwarya, a duk lokacin da na kalli almarijirai na gansu suna yawo kamar wadanda ba su da iyaye, talauci, rashin wadata, da kuma rashin damuwar wane irin hali za su shiga a wannan almajirancin. Kiran da zan yi ga iyayen yaran shi ne, ya kamata su san cewar shi yaro yana bukatar a kula dashi sosai, ko da ka na son ka turasu almajirancin, to ka turasu garin da wani na ka yake, yadda zai dinga lura da shi yana ganin yadda yake tafiyar da mu’amalarsa, amman gaskiya banda kananun yara wanda basu wuce ‘6-10years’ ba, idan almajirancin ne a tura wanda suka mallaki hankalin kansu, kuma za su iya neman na kansa. Babu wani amfanin tura yara almajiranci, sai ma rashin amfaninsa, saboda tura yara kanana almajiranci ya gurbata rayuwarsu. Hanyar daya ce nake gani, iyaye su hakura su daina tura yara kanana almajiranci.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Ra’ayoyinku Kan Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu A Kano Bayan Kisan Hanifa

Next Post

Yadda Za Mu Koya Wa ‘Ya`yanmu Tausayi Da Son Junansu

Labarai Masu Nasaba

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

by Rabi’at Sidi B.
5 days ago
0

...

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

by Rabi’at Sidi B.
2 weeks ago
0

...

Sallah

Tsokaci Game Da Sabon Salon Da Za A Ci Bikin Sallah Da Shi Bana

by Rabi’at Sidi B.
3 weeks ago
0

...

Tsokaci A Kan Yadda Matasa Ke Raya Al’adar Tashe A Zamanin Nan

Tsokaci A Kan Yadda Matasa Ke Raya Al’adar Tashe A Zamanin Nan

by Rabi’at Sidi B.
4 weeks ago
0

...

Next Post
Tausayi

Yadda Za Mu Koya Wa ‘Ya`yanmu Tausayi Da Son Junansu

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

 

Loading Comments...
 

    %d bloggers like this: