Almajirci: Siyasa Da Gaskiyar Lamarin (II)

arabiandokaji@gmail.com   08135353532

Rubutuna na makon da ya wuce mai taken “Almajirci: Siyasa da gaskiyar lamarin” ya ja hankali mutane iri daban-daban. Na samu kira da dama a waya, da kuma gajeru da dogayen sharhuna ta akwatin sakona na yanar gizo. Wasu kuma sun tuntunbe ni ta kafar Facebook da ra’ayoyinsu game da abin da na bayyana. Da dama daga cikin masu sharhin sun ce lallai, tilas na yi bayanin abin da littafin da na fada na Tarihin Malam Mahmudu Koki ya kawo saboda dalilin cewa littafin zai wuyar samu ga mutane da dama. Magana ta biyu da ta ja hankalina, ita ce sharhin wani ma’aikacin kungiyar kula da koken jama’a ta gwamnatin tarayya (Public Complaints Commission) akan cewa idan ma fa da zamani, to da sakacin Bahaushe shi ma. Rubutuna na yau zai mayar da hankali ne wurin bayani akan wadannan batutuwa da ma wasu da ban fada ba.

Littafin Tarihin Malam Mahmudu Koki wanda shahararren marubucin nan Neil Skinner ya wallafa, tarihi ne da Marigayi Malam Mahmudu Kokin ne da bakinsa ya bada shi. Na sallada misali da rayuwar malam Mahmudu Koki ne saboda yayi almajirci ne daf da rushewar jiyan Bahaushe da farawar yau din sa ta zama a kan wayewar Bature. An haife shi a garin Kano a lokacin yakin Basasa Yusufawa da Tukurawa, da wayonsa Bature ya zo kasar nan, kuma da ransa Bature ya bar kasar nan. Ya rasu a shekarar 1974. Ya ga jiya, kuma ya ga yau! Malam Mahmudu Koki yayi bayanin rayuwarsa daki-daki. A ciki yayi tsokaci akan yadda rayuwar almajiri mai neman ilimi ta ke a Kano kafin zuwan Bature. Babu batun yunwa ga almajiri me karatu domin kullum almajirai basa rasa abin da za su saka a bakin salati, saboda akwai wadata ba yunwa da talauci.

Da fari dai tsangayun da ake zuwa karatu a kauye ko maraya yawancin su suke, ba kamar yanzu da ake zuwa birni ba. Tsangayu kamar na Ringim da Tsakuwa sun shahara kwarai. Kamar yadda Alhaji Mahmudu ya nusashe mu, ana zuwa karatu ne tsangayun da aka san abinci baya wahala. A tsarin Bahaushe, almajirai da suka bar gidajen iyayensu don karatu abin girmama wa ne. Ciyar da su gata ne ga al’umma, ba kamar yanzu da ake ganin hakan a matsayin taimako ba. Al’ummar ta damu ta gina rayuwar su, domin sune masanan gobe da za su bawa bayanta alkibla. Zamani bashi da wannan damuwar.

Daga hanyoyin da suke samun abinci akwai ciro. Idan akai girbin albarka irin su gyada ko rogo, misali, idan aka cire abin da aka samu, ba a damu da hake ramin har sai an ciro duka sauran ‘ya’yan da su ke kasa ba. Iya abin da aka ciro na jikin tushiyar ya isa saboda wadata. Irin wannan ragowa dake zubewa a kasa da kuma wadda take kasa, ita almajirai ke zuwa su diba. A rana, mutum kan tara kwano daya ko fin haka. Lallai kam! Jiya ba yau ba!

Sauran hanyoyin da ake samun abincin ya hada da abincin sadaka da jama’ar gari ke kawowa domin ciyar da almajiran fisabilillahi! Yara daga cikin almajiran na debowa matar malam ruwa, ko su yi mata ita ce, ita kuma sai ta basu abinci idan ta dafa. Wasu kuma na taya malamin su noma ne, idan an girba sai a dinga ci da su. A tsarin wannan karatu ba’a biyan kudin makaranta, saboda karatu kyauta ne. Idan malami yaga alamar almajiran sa basa samun tallafin abinci, sai ya bar garin ya koma wani. Yan gata, musamman wadanda aka kawo karatu daga cikin birni, iyayensu na aiko musu da kayan abinci. Idan kuma iyaye suka fahimci malami baya kula da karatu da tarbiyar yaran su da suka kawo masa, sai su dauke su daga tsangayarsa su kai su wata. Idan kuma gaba zai kara, zai tura kowa gidan su ne, kana ya aikawa iyayen ya ji ko dan su ya zo gida.

Talaucin zamani, ya sa mutane na tasowa daga kauyuka zuwa birane domin karatu ko kasuwanci. Babu komai a kauye, domin harkar noman kanta ta lalalce. Duk wani abu da ake bukata da za’a iya amfani da shi a gina rayuwa mai nagarta yana birni. Wannan tasa kullun burin mutumin kauye ya taho birni! Rashin yadda za su yi da tarin ‘ya’yan da suke da su yasa mutanen kauye na turo ‘ya’yen su birni domin neman mafitar rayuwa. Matukar gwamnati ba za ta duba halin da kauyuka suke ciki ba, tabbas kuwa kawo yara birni a jibge yanzu aka fara shi. Babu komai a kauye sai wahala, ba kuwa wanda yake son wahala a duniyar nan!

Idan muka koma kan cigaban rubutun mu na wancan makon, shin wai mene gaskiyar adadin almajiran da ake fada akwai a Arewacin kasar nan! Ba nufina na nuna cewa ba’a fama da matsalar alamajirci ba. A’a, ina so ne na nuna cewa akwai siyasa a al’amarin fiye da yadda muka fahimta. Yawancin ma su kiyasi na cewa akwai almajirai tsakanin miliyan bakwai zuwa goma (7-10) a Arewacin kasar nan. Idan wannan haka ne, magana ake ta almajirai kwatankwacin adadin mutanen jihar Kano gaba dayanta a Arewa! Anya kuwa wanan lissafin haka ne?

A iya bincike na, na kasa samun unguwa guda daya a Kano da take da almajirai guda dubu biyu! Kiyasi ya nuna ba inda ya kai Kano yawan alamjirai da mabarata, to idan a Kano babu unguwar da take da alamajirai da mabaratu dubu biyu, to a ina aka samu lissafin miliyoyin da ake? Sau tari mutun kan rasa inda kiyasan da ake fitarwa a kasar nan su ka dosa? Misali, ance kullum a Kano ana shan miliyoyin kwalaban maganin maye. Tambayar a nan ita ce, ance kusan kaso saba’in (70) na yan Nijeriya na samun k’asa da Dala daya ($1) a rana, tunda ance Arewa ta fi ko ina talauci a k’asar nan (musamman Kano da aka ce tafi kowa yawan mabarata da almajirai!), a ina ake samun kudin da ake shan maganin mayen da ya kai kusan Dala hudu ($4), wato ninki hudu (4) na abin da kaso saba’in (70) na Yan Nijeriya ke samu a rana!

Almajiran nan ance birane su ke shigowa, birane nawa ne gaba daya a Arewacin Nijeriyar da za’a iya zuwa barar? Wannan ma fa idan muka dauki cewa almajirai da mabarata daya ne kenan! Anya kuwa babu wata magana a kasa ta kokarin bakanta Bahaushe a idon duniya? Shin wannan rashin zuciya na Bahaushe da nuna halin ko in kula da yake akan abubuwan da suka shafe shi zai haifar masa da mai ido? Babu wata manufa da wadannan kungiyoyi masu zaman kan su ke da shi suke fakewa da maganar almajirai? Ba wanda ya damu da cewa ta iya yiwuwa suna bukatar shigo da kudade kasar ne a kan kari don wata bukata ta daban, shine ake fakewa da guzuma ake harbin karsana? Dan dan dan dan dan dan, wai Bazazzagi ya hau jirgin kasa!

Akwai bukatar gwamnati da jama’ar gari su daina siyasa da wannan al’amarin. Kungiyoyin masu zaman kan su tilas su kula da irin kwangilolin da ake ba su akan al’umman su da kuma kasar nan! Sa ran wani zai magance mana matsalolin mu babban kuskure ne. A daya hannun, yawan aure-aure da Bahushe ke yi, ya haifi ‘ya’yan da ba shi da yadda zayyi da su ba zai haifar masa da mai ido ba. Tilas ya tashi ya karbi chanjin da zamani ya zo da shi, in ba haka ba zamani ya ci gaba da barin sa a baya! Jiya ba yau bace.

Babu sabon karatu duk a wadannan maganganun da ake kawo masa, domin sama da shekara hamsin (50) da suka gabata, Malam Sa’adu Zungur a wakarsa ta ‘Arewa Jamhuriyya ko Mulukiyya’ ya zayyana su. Dabi’un Bahaushe na rashin kishin kai, rashin zumunci, bara, roko, gori, zambo, son banza, son kai, hassada da kin karatu da son sharholiya na daga cikin abin da ke dakile ci gabansa. Ko da yake, yanzu yana chanjawa, musamman a bangaren karatu. Yawancin almajirai sun dukufa da karatun boko!

 

 

Exit mobile version