Muhammad Awwal Umar" />

Almundahana: Kotu Ta Umarci A Kamo Tsohon Gwamnan Neja

Kotun daukaka kara ta tarayya mai mazauni a minna ta janye belin da aka baiwa tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu tare da dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar PDP, Alhaji Umar Muhammad Nasko, hukuncin janye belin ya biyo bayan wani zaman da kotun tayi ranar alhamis 23 ga watan nan kan tuhumar tsohon gwamnan da dan takarar kujerar gwamna a inuwar PDP kan alhumdahanar kudaden gwamnatin jiha a lokacin da suke karagar mulkin jihar.
Mai shari’a A. B Aliyu wanda ya jagoranci zaman kotun ya nuna fushinsa na rashin halartar wadanda ake tuhumar daga su har lauyoyin da ke kare su wanda yace wannan na nuna rashin mutunta umurni kotu daga wadanda ake tuhumar.
Karar dai wadda hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa ( EFCC) ta shigar a kotun tana tuhumar mutanen biyu, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu da Alhaji Umar Muhammad Nasko da hannu akan almundahana da kudin gwamnati kusan naira biliyan biyu da kuma wasu tuhume-tuhume na wasu laifuka na sama da fadi da kudaden gwamnati.
Wadanda ake tuhumar tunda farko an gurfanar da su a gaban mai shari’a Yelin Bogoro, inda bayan kammala bincikensu ba ta iya samun su da laifi ba, sai dai mai shari’a Bogoro ta mayar da su wata kotun dan yin bincike da bin bahasi.
Mai shari’a Yelin ta gabatarwa ta umurci mai shari’a Aliyu da ya saurari karar kuma ya binciki zarge zargen da ake yima wadanda ake tuhumar. Bayan bijirowar maganar, a yau alhamis ba daya daga cikin wadanda ake tuhumar da ya halarci zaman kotun.
Lauyan daya daga cikin wadanda ake tuhumar, Mista Osuman Mamman ( SAN) yace sun rubutawa kotun cewar zasu halarci zaman kotun sauraren karar zabe, kuma bai samu damar tura lauyan da zai wakilce shi a zaman babbar kotun ba.
Mai shari’a Aliyu dai ya janye belin da aka baiwa wadanda ake tuhumar tare da bada umurnin rubuta masu sammaci dan sake kamo wadanda ake tuhumar.
Kotun ta dage cigaba da sauraren karar zuwa ranar littinin 27 ga watan Mayun 2019.

Exit mobile version