Connect with us

RAHOTANNI

Al’umma Sun Goyi Bayan Takarar Abubakar Ismaila Isa Na Zama Gwamnan Katsina

Published

on

Gamayyar magoya bayan dan takarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Malam Abubakar Ismaila Isa, sun bayyana dalilan da ya sa suke son Malam Abubakar Ismaila Isa ya zama Gwamnan jihar Katsina.

Gamayyar magoya bayan sun bayyana haka ne lokacin da suke zantawa da manema labarai a Katsina cikin wannan mako.

Mai magana da yawun gamayyar magoya bayan, Alhaji Abdullahi Usman Arawa ya bayyana cewa Malam Abubakar Ismaila Isa mni, ne ya fi cancanta da ya zama Gwamnan jihar Katsina a zaben da ke tafe a shekarar 2019. Alhaji Abdullahi, wanda jigo a jam’iyyar APC ta jihar Katsina, ne ya bayyana haka ga manema labarai da ya yi a garin Katsina.

Alhaji Abdullahi Usman, wanda a shekarar 2011 jigo ne a tafiya Gwamna jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari. Ya bayyana cewa Malam Abubakar Ismaila Isa matashi ne da ke da wayewa da kuma ilimin tafiyar da mulkin al’umma tare da kwarewa yadda ya kamata a fannin iya gudanar da mulkin al’umma.

Ya bayyana cewa, jihar Katsina na bukatar Gwamna matashi da ke da jini a jika yadda zai iya magance matsalolin da suka addabi jihar.  Don haka ya ce, gwaninsa mutum ne da ya ke da tausayi da rikon amana da kuma gogewa kan sanin makamar mulki ta kowace fuska. Sannan kuma gashi da jini a jika wanda zai bashi damar gudanar da aiki dare da rana. Sannan ya kara da cewa, Malam Abubakar Ismaila Isa yana da kwarewa ta fuskar tattalin arziki, don haka zai yi duk abin da ya kamata wajen ganin ya ceto jihar Katsina daga halin da take ciki na durkushewa saboda mulkin kama-karya da ake yi a jihar yanzu. Ya ce, shi daya ne tilo da jihar Katsina da ta yi alfahari da shi idan ya zama Gwamnan jihar a zaben da ke tafe.

Alhaji Arawa, ya kuma bayyana cewa, matukar jam’iyyarsu ta APC na son cin zabe a jihar Katsina to wajibi ne ta tsayar da Malam Abubakar Ismaila Isa a matsayin dan takarar Gwamnanta. Ya ce idan kuma aka yi son rai wajen tsayar da wanda bai cancanta ba to za a sha mamaki a wajen talakawa. Don haka ya nemi jam’iyyar APC a jihar da ta bai wa Malam Abubakar Ismaila Isa takarar Gwamnan jihar Katsina a zaben 2019. Ya ce, wajibi ne ‘yan jam’iyyar APC a jihar su tabbatar cewa sun zabi Malam Abubakar Ismaila Isa a zaben fid da gwani na jam’iyyar da za a yi cikin wata mai zuwa.

Ya kuma yaba wa shugabannin jam’iyyar APC na kasa bisa yadda suka dage sai an yi kato bayan kato a zaben fid da gwani na jam’iyyar. Ya ce hakan zai taimaka kwarai wajen bai wa ‘yan jam’iyya damar zaben wanda suke so don ya yi musu takara. Ya ce, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshimohole ya yi namijin kokari wajen dawo da martabar jam’iyyar a irin wannan lokaci na ake cikin shiga babban zabe. Sannan ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su baiwa shugaban jam’iyyar goyon baya don ganin ta lashe dukkan zabukan da za a yi a shekarar 2019.

Malam Abubakar Ismaila Isa na da kudurori da daman gaske don ganin ya fidda Katsinawa daga cikin halin da suke ciki na rashin isassun kayan more rayuwa da suka zama abin bege ga al’ummar jihar Katsina. Katsinawa na burin ganin rayuwarsu ta inganta musamman a irin wannan lokaci da suka yi sa’ar ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari ne shugaban kasa kuma dan asalin jihar ce. Don haka Al’ummar jihar Katsina na da tabbacin cewa za su sami dukkan abubuwan da suke bukata na rayuwa matukar shugaban Buhari na shugaban kasa kuma Malam Abubakar Ismaila Isa ne Gwamnan jihar Katsina.

Ya bayyana cewa jihar Katsina ta zama koma baya saboda rashin iya jagoranci na shugabanni da ke mulki yanzu. Ya yi mamakin yadda aka kasa yin aikin komai a jihar. Ya ce Idan aka kwatanta mulkin Gwamnatin jihar Katsina na shekaru uku za a ba da a yi aikin komai ba.Ya kuma na da misali da wutar lantarkin garinsu da ya lalace shekaru uku za suka wuce amma har yanzu Gwamnatin jihar Katsina ta kasa gyarata. Ya ce sun yi duk abin da ya kamata su yi, sun yi Don ganin Gwamnatin jihar Katsina ta gyara musu wutar lantarkin da ba za a kashe sama da naira miliyan daya ba. Amma an kasa gyarata.

Ya ce tashar teku ta jihar Kaduna an kammala ta, amma har yanzu wadda aka fara a Funtuwa an kasa kammala ta saboda jihar Katsina ba ta da kudeden da za ta zuba don kammala wannan aiki. Kamar yadda Gwamnan jihar ya bayyana. Ya ce wannan rashin iya shugabanci ne. Domin Gwamnatin jihar na da kudaden da za su iya kammala wannan aiki amma ta ki yin aikin. Ya ce wannan ya nuna Gwamantin ba ta san muhimmancin wannan tasha ba da ake kira Dry Port a Turance GA al’ummar jihar.

Ya ce tun bayan da jihar Katsina ta sami jihar ta a shekarar 1987 ta yi gwamoni da daman gaske tun daga na mulkin soja har zuwa ga na farar hula. Ya ce amma ba a yi wata Gwamnati mara alkibla ba irin wannan Gwamnanin.

Alhaji Abdullahi Arawa ya bayyana cewa lokaci ya yi da al’ummar jihar Katsina za su farka daga baccin da suka dade suna yi. Ya ce dole a wannan lokaci su tabbatar da sun zabi mutanen da suka cancanta a kan dukkannin kujerun da za a yi takararsu a zaben da ke tafe a shekarar 2019.

Ya ce Gwamnatin jihar Katsina ta gaza a dukkannin bangarorin mulki. Ya ce duk wanda ya yi jam’iyyar APP zuwa ANPP zuwa CPC, to babu dalilin da zai zabi masu mulki a jihar Katsina yanzu. Saboda sun kauce daga tafiya irin ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga cikin kudurorin, Malam Abubakar Ismaila zai tabbatar ya ci gaba da yin zaben Kananan Hukumomi a jihar. Don haka ne zai rage matsanancin talauci da ake fama da shi a jihar. Zai kasance mai bin doka da oda ta hanyar gudanar da zaben Kananan Hukumomi da zarar wa’adin mulkinsu ya kare ba tare da yin kantomomi ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Zai dawo da biyan kudin jarabawar kammala karatun sakadare ta WEAC da NECO ga ‘yan jihar, wanda wannan gwamnati ta janye biya musu. Hakan zai taimaka wajen ragewa iyayen da ba su da karfin biyan kudin wahalhalun da suke fada da su. Sannan zai ci gaba da biya wa daliban jihar kudaden yin karatu a kasashen waje.

Ya ce akwai hanyoyi da dama da gwamnatocin baya suka yi a jihar Katsina, amma yanzu duk sun lalace. Wannan gwamnati da ke mulki yanzu ta kasa gyarasu. Baya ga wannan ya ce akwai abubuwa da suka lalace a jihar Katsina da wannan Gwamnatin ta kasa gyarasu. Don haka ya zama wajibi al’umma su kauda wannan Gwamnatin su musanyata da Gwamnatin Malam Abubakar Ismaila Isa, wadda za ta kawo gyara a jihar.

karshe Alhaji Abdullahi ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su zabi Malam Abubakar Ismaila Isa a matsayin Gwamnan jihar Katsina. Ya ce matukar suka zabi Abubakar za su ga aikin da ba su taba gani ba a jihar Katsina. Ya ce zaben Malam Abubakar Ismaila Isa ne kadai mafita ga al’ummar jihar Katsina.

Ya ce za su yi bakin kokarinsu don ganin sun kawar da ‘yan baranda a Katsina da kuma musanyasu da Malam Abubakar Ismaila Isa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: