Al’umma Sun Yaba Da Kokarin Kantomar Karamar Hukumar Giwa

Exif_JPEG_420

A kokarin shayar da jama’a romon dimokradiyya, Al’ummar karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna yabo suke ga kantomasu bisa yadda yake kawo wa karamar hukumar na ci gaban rayuwa ta bangarori da dama musamman aikin samar da kyakyawan kiyon lafiya.

Wakilinmu ya sami damar zuwa karamar hukumar don ji da ganin abin da al’ummar take yabo a kai.

Abu na farko da wakilinmu ya yi kacibis da shi shi ne, wata gonar itace mallakar karamar hukumar mai Suna (NONI FARM) da kantomar karamar hukumar ya kirkira don anfanin jama’ar karamar hukumar jihar Kaduna baki daya.

Bayan wakilin namu ya gama nazari a kan wannan gona sai ya nufi cikin gari a can kuma sai ya riski wani karamin kamfani na tara ledoji da robobin da jama’a ke zubarwa a bola shi ma mallakar karamar hukumar.

Wannan dalilin ya sa wakilinmu ya koma sakateriyar ta karamar hukumar don jin ta bakin Kantoma game da wadancan muhimman abubuwa guda biyu da ya yi kacibis dasu a yayin shigowar sa.

Honorabul Dakta Yahaya Sale Ibrahim, shine kantomar karamar hukumar, ya yi karin haske game da wancan kokari da mutane ke nuna godiyarsu akai inda ya fara da mika godiyarsa ga Allah subahanahu wa ta’ala bisa yadda ya sami kyakkyawar shaida daga mutanen karamar hukumar bayan haka kuma sai ya kada baki yace, “Gonar (NONIFARM) gona ce da na kirkira sakamakon ziyarar da na kai wata kasa da suke amfani da wannan itaciya mai dauke da sinadarai masu dama da ke maganin cututtuka iri-iri da suka hada da ciwan kanjamau da tarin Lala ko tarin Kika da yara kan fama da shi wanda akwai yadda ake sarrafa itaciyar da an bai wa yaro mai tarin (LALA) ko tarin (KIKA) da mai dauke da ciwon sida wato HIB to a kan sami dacewa.

Honorabul ya ci gaba da cewa hakan yasa ya kawo wannan itaciya don amfanar jama’ar kuma ya ce abin mamaki shi ne yadda jama’ar karamar hukumar suka bada hadin kai a kan ganin wannan gona ta ci gaba.

Ganin yadda jama’ar suka bani wannan hadin kai da goyan baya hakan yasa ya kara yin wani tunani a kan kawowa karamar hukumar hanyar samun taro da sisi in da na kirkiro karamin kamfanin da zai rika sarrafa ledojin da jama’a suka gama amfani da shi suka zubar a bola, kamfanin zai rika tsintar ledojin ne yana tarawa bayan an samu sai  a mayar da shi wani abin kamar buta da bokitin roba da muka saba anfani da shi a wajan wanka ko yin alwala da dai sauransu kuma lokaci guda an rage wa gari datti wanda lokuta da yawa dattin ne kan haifar da bullowar cututtukar da suke addabar mutane.

 

Exit mobile version