Zubairu T M Lawal" />

Al’umman Nasarawa Na Amfana Da Likitan Talakawa

Dubban alumman ne suke cin gajiyar kwararen Likitan nan da ake wa lakabi da Likitan Talakawa Honarabul Joseph Haruna Kigbu, ta hanyar bada magunguna da kumayin Tiyata ga marasa lafiya kyauta. Duk da cewa wanan ba farkon al’amari bane ga Honorabul Joseph Haruna Kigbu wajen taimakawa dubban alumma a fannin kiwon lafiya ba.
A bana ya kaara fadada wanan shirin day a kwashe tsawan shekaru 20 yana baiwa Talakawa agajin magunguna da Tiyata kyauta.
A makon da yagabatane Honorabul Joseph Haruna Kigbu a gabatar da wannan tallafin a karamar hukumar Toto da jihar Nasarawa yadda dubban alumma maza da mata suka samu wanan tallafin cikin wadanda suka samu halartan wanan tallafin sun hada da tsohon Gwamnan jihar Nasarawa Satana Abdullahi Adamu inda ya yaba da wanan tallafin na kiwon lafiya da tawagar Honorabul Joseph Haruna Kigbu ta Doctor on the Mober Africa ke badawa.
Sanata Abdullahi Adamu yace hakika jihar Nasarawa tana alfahari da wanan tawagar ganin yadda tawagar ke bada gudumawa a kasa baki daya. Kuma amfanin ilumi kenan ayi aiki dashi. Sanatan yayi kira ga alumma dasuyi koyi da irin wanan bawan Allah da yake taimakawa alumma a bangaren kiwon lafiya.
Ya kara da cewa babu abinda mutum zai baka wanda ya wuce kiwon lafiya.
Baya ga nan tawagar ta saua a karamar hukumar Karu kamar yadda ya gudana a karamar hukumar Toto nan ma a kwashe kwanaki uku ana gabatar da wanan tallafin ga alumma marasa rinjaje maza da mata da yara. Shirin bada magani kyauta ya farane tun daga ranar Lahadi zuwa Laraba .
Bayan kamalawan ne tawagar ta sake sauka a karamar hukumar Lafia inda aka fara gabatar da shirin a garin B.A.D shima ana saran samada mutum dubu uku zasu samu tallafin kiwon lafiya kama daga magunguna zuwa Tiyata .
Haka zalika tawagar ta hada da karamar hukumar Obi inda shima za’a kwashe a kalla kwanaki uku ana gabatar da wanan aikin na kiwon lafiya kyauta. Ana saran suma a samu sama da mutum dubu uku.
Da yake jawabi ga manema Labarai Honorabul Joseph Haruna Kigbu yace; wanan ba sabon abu bane gareshi, a kullu burinsa yaga Talakawa suna walwala. Ya kara da cewa; ba zai manta da Talakawa ba saboda shima iyayansa talakawane kuma suna sha wahala a rayuwa sosai . yace, bayan mutuwar mahaifinsa mahaifiyarsa itace ta rikayin kwadago tana biya masa kudin makaranta .
Yau Allah yasa ya zama wani abu mai ya kamata yayi? Idan har ba zai rika tuna baya ba. Ya kara da cewa ya godewa Allah daya bashi wanan zuciyar yake tunawa da na kasa dashi. ‘Ya kara da cewa na tabbata talakawa suna kaunana ‘ saboda duk lokacin da na fito takara suan zabata ban taba tsayawa takara na fadi ba sai dai idan naci zabe ayimin murdiya karfi da yaji.
Ya kara da cewa” a 2011 munci zabe a matakin Majalisar wakilai kuma alumma sunga abinda mukayi masu a shekara hudu da mukayi a majalisa shi yasama da muka sake tsayawa suka zabeni a matsayin na koma na maimaita, amma Gwamnati ta kwace mana mukayi hakuri mukabarwa Allah sai gashi a wanan shekararma da muka sake tsayawa takara munci zabe duk da cewa anyi mana irin wancan amma mun tabbata Allah zai maida mana da nasararmu.

Exit mobile version