Daga Abubakar abba, Kaduna
kungiyar Al’ummar garin Afaka (TAC) dake a karamar hukumar Igabi a cikin jihar Kaduna da kuma al’ummar mazabar ta Afaka sun jajanta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ga rasuwar babban direbansa Saidu Afaka.
“Muna son yin amfani da wannan damar domin jajanta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ga rasuwar babban direbansa Saidu Afaka”.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Daraktan yada labarai na kungiyar Malam Ibrahim dahiru danfulani ya fitar a jihar Kaduna.
kungiyar Al’ummar garin Afaka ta kuma yiwa iyalan mamaci, ‘yab uwansa da kuma abokansa ta’aziyar rasuwarsa, inda suka yi nuni da, rasuwar ta sa, babban rashin ne ga yankin na su na Afaka.
A cewar kungiyar,” rasuwarsa, babban direban Saidu Afaka, babban rashin ne Ba wai ga iyalansa ba Har da daukacin al’ummar ta Afaka ganin cewa ya fito ne daga yankin na Afaka”.
Sun bayyana cewa, rasuwar marigayin babban rashi ne ga daukacin al’ummar dake a yankin, inda kuma suka yi addu’ar Allah ya gafarta masa tare da bai wa iyalansa, ‘ykn uwansa da kuma abokansa juriyar rashin sa.
Babban abinda za a yi saurin tuna wa da marigayin Saidu Afaka, shi ne yadda a lokacin aikin hajji na shekarar 2016 a kasar Saudiyya, marigayi Saidu ya tsinci wata jaka shake da kudaden kasar waje amma ya kai jakar ga Hukumar Alhazai ta kasar nan domin ayi cigiyar mai jakar, inda hakan ya sa, mahukuntan kasar ta Saudiyya ta yaba masa kan wannan halin na gari da ya nuna.
Marigayi Sa’idu Afaka, ya rasu ne Asibitin Fadar Shugaban kasa a ranar talatar da ta gabata bayan bayan rashin lafiya .