Al’ummar Barwa Sun Yaba Wa Minista Sadiya Saboda Rijiyar Burtsatse Da Asibiti

Barwa

Daga Umar Hunkuyi

Al’ummar kauyen Barwa da ke Yankin Birnin Tarayya (FCT) sun yaba wa Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya saboda ta gina masu asibiti da rijiyar burtsatse don samun ruwan sha.

Mai unguwar kauyen, Cif Monday Kogi, shi ne ya furta yabon a  lokacin da Minista Sadiya Umar Farouk da wasu jami’an ma’aikatar su ka je Barwa domin kaddamar da bikin Ranar Magance Fatara ta Duniya ta shekarar 2020 wanda aka yi a ranar Asabar.

Cif Kogi, wanda ya bayyana godiya ga Gwamnatin Tarayya, ya tuno da cewa kauyen ba ya da ruwan sha da asibiti har sai da ma’aikatar ta kai masu ziyara a bara.

Ya ce: “Tun zuwan ku na farko a ranar 17 ga Oktoba, 2019, mun ga yadda aka gina mana rijiyar burtsatse da asibiti a kauyen Barwa. A madadin jama’ar Barwa, mu na maku godiya.”

Shugaban al’ummar ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta katange asibitin kuma ta gina hanyar zuwa kauyen daga filin jirgin sama.

A jawabin ta, Hajiya Sadiya Umar Farouk, wadda Daraktan Harkokin Agaji, Mista Ali Grema ya wakilta, ta ce ta yi murna da kaddamar da bikin Ranar Magance Fatara ta Duniya a wannan kauyen.

Ta kara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki da hukumomin da ke karkashin ta don tabbatar da an cimma burin Shugaban Kasa na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga fatara a cikin shekara 10.

Ta ce, “Wannan rana ta musamman ta bada dama a fahimci irin kokari da faman da mutane masu fatara ke yi da kuma damar su fadi abin da ke damun su.

“An shafe shekaru ana yaki da fatara a yayin da kashi arba’in cikin dari na al’ummar Nijeriya su na rayuwa ne cikin kunci kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana. Daya daga cikin manyan ayyukan gwamnati shi ne a taimaka wa dukkan jama’a kuma a ba su kariyar da ta dace domin yaki da fatara abu ne da ke cikin ran gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

“Wannan gwamnatin ta kasance mai sadaukarwa ga manufofi da tsare-tsaren kula da mutane masu karamin karfi na duniya kuma za ta yi aiki da manufofin kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya.”

Ita dai Ma’aikatar Harkokin Agaji, ta zabi kauyen Barwa ne a matsayin inda za ta fara wannan bikin na Ranar Magance Fatara ta Duniya a bara tare da taimaka wa kauyen ta hanyar gina masu wurin shan magani da kuma sama masu wurin dibar ruwan sha ta hanyar shirin taimakon al’umma, wato ‘Community and Social Debelopment Project’ (CSDP).

A bana, ma’aikatar ta bada kyautar wuraren wanke hannu guda uku da kayan wanki da su ka hada da sabulai, kyallayen rufe fuska da magungunan tsaftace hannu ga iyalai, da kuma tukunyar jama’a  saboda wannan ranar, a yayin da ministar da sauran jami’ai su ka yi wankin hannayen su na gwaji ga jama’a.

Jigon bikin na bana dai shi ne “Aiki Tare don Cimna Adalcin Al’umma da Yanayi ga Kowa” (Acting Together to Achiebe Social and Enbironmental Justice for All).

Exit mobile version