Connect with us

SIYASA

Al’ummar Bichi Na Goyon Bayan Takarar Injiniya Abubakar Kabir Abubakar

Published

on

Al’ummar karamar hukumar Bichi na cigaba da nuna goyon bayansu da fitowa neman takarar majalisar wakilai ta tarayya da Injiniya Abubakar Kabir Abubakar yayi domin neman wakiltar karamar hukumar a karkashin inuwar jam’iyyar APC sakamakon irin ayyukan kyautatawa da yake a yankin.
Cikin wadanda jaridar Leadership A Yau ta zanta dasu a karamar hukumar sun nuna cewa takarar ta Injiniya Abubakar Kabir ta mai kamar zuwa ne kan aika duba da irin gudummuwa ta cigaba da yake bayarwa wajen taimakawa cigaban al’umma.
Musamman ma yadda kullum yake tallafawa cigaban matasa ta fannin taimakawa wajen cigaban ilimi ta biya musu kudin rijistar makaranta da saya musu takardun neman shiga manyan makarantu da biya musu kudin daukar jarabawa sannan da basu tallafi domin dogaro dakai wanda yake a cikin lunguna da sakuna na garuruwan karamar hukumar Bichi.
Al’ummar na Karamar hukuma Bichi sun kuma yaba da cewa Injiniya Abubakar Kabir Abubakar Bichi yana gyara masallatai da gina sabbi da sayan fili sukutum guda a mai dashi makabarta da kuma gyara da gina makarantun islamiyya sannan kuma yana bada tallafin abin sayen magani ga marasa lafiya.
IA irin wannan taimako da yak enema ga marasa lafiya ya dauki nauyin wani mara lafiya wanda ya kashewa tsabar kudi sama da N1,000,000 banda wanda yake ba’a sani ba domin shi mutumne mai yawan alheri da tausayi da kyautatawa.
Da dama al’ummar Bichi da muaka zanta dasu sun ce bias la’akari da abubuwanda suke gani a kasa na kulawa da al’umma da Injiniya Abubakar Kabir Abubakar Bichi ga al’ummarsu a shirye suke su bashi hadi kai da goyon baya dazai kaishi ga nasara r wakiltarsu a majalisar wakilai ta tarayya ba batun jam’iyya bane Magana c eta wanda yake damuwa da damuwar al’umma.
Sai dai sun yi kira gay an siyasar yankin masu zaben fidda gwani suyi abinda yakamata wajen zabar mutane irinsu Injiniya Abubakar biassa la’akari da cancantarsa da gudummuwa da yake ga ci gaban Bichii a karan kansa balle ma ace an zabeshi a wannan matsayi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: