Ibrahim Muhammad" />

Al’ummar Bichi Suna Goyon Bayan Yan Takarar APC —Lawan Shehu

Anyi kira ga al’ummar jihar Kano su baiwa Gwamnan jihar Kano Dkt.Abdullahi Umar Ganduje da sauran yan takara na mataikai daban-daban hadin-kai da goyon baya a dabe mai zuwa dan ganin an sami nasara cin zabe dan dorawa akan ayyukan alkhairai da akewa jihar Kano.Dan takarar majalisar jaha a karkashin jam;iyyar dan wakiltar karamar hukumar Bichi.Tsohon dan majalisar tarayya daya wakilci karamar hukumar.Alhaji Lawan Shehu yayi wannan kiran da yake zantawa da manema labarai.
Yace al’ummar Kano su nuna godiyarsu ga Allah ta ni’ima da yayi musu duba da irin abubuwa na ayyuka da Gwamna Ganduje yayi a birni da karkara a kuma yabawa Ganduje ta sake bashi kuri’u na goyon baya a wannan takara da yake karo na biyu domin ya maimaita ya sake dorawa akan muhimman ayyuka daya faro domin cigaban al’umma.
Ya yi nuni da cewa al’ummar karamar hukumar Bichi sun gamsu da Gwamna Ganduje kuma duk wani mutum mai kishi dake son cigaba da sanin yakamata ,taimakekeniya karamci,kulawa zai yiwa Allah godiya da Gwamna Ganduje domin al’ummar yakin sun gani sun taba sun taka ayyukan hanyoyi da dama da Gwamna Ganduje yayi cikin garin Bichi da kauyukanta.
Alhaji Lawan Shehu wanda har ila yau tsohon shugaban karamar hukumar Bichi ne yace Gwamna Ganduje yana aiki dan samawa al’ummar Bichi matsalar ruwansha anata aikin jawo ruwa sanna ga manyan tankuna da akasa guda biyu a tsakiyar garin da gefen garin da ake tara ruwa wanda yakan dauki lokaci ana amfani dashi a garin ga kuama hanyoyinda akayi harda wacce ta tashi daga Ganduje zuwa Saye, akwai wacce akayi daga Maitsidau,wajila zuwa makoda.
Dan takarar na majalisar jaha yayi nuni da cewa a baya takarar majalisar tarayya daya baro yake sake nema,amma saiya sami kansa a takarar majalisar jaha,kuma a matsayinsa na musulmi ya yarda da kaddara duk yanda yazo masa ,duk abinda akeso in bashi Allah ya zabawa mutum ba zabin Allah shi yafi,shine makasudinda yasa yabar takarar tarayya yak eta majalisar jaha.
Lawan Shehu yace takarar tasa ta samu karbuwa sosai a tsakinin al’ummar karamar hukumar Bichi domin sun san irin abubuwa da yayi musu a baya lokacinda yayi shugabancin karamar hukumar da kuma majalisar tarayya daya wakilcesu dan haka mutane sun gani sunada yakinin za’a dora akan abinda akayi harma fiyeda na baya idan aka kai ga nasara Shima wanda yake takarar majalisar tarayya injiniya Abba mutumne matashi da yake kulawa da cigaban al’umma da abinda Allah yah ore masa wannan na daga dalilan karbuwarsu.
Alhaji Lawan Shehu Bichi yace a halinda ake ciki jam’iyyarsu ta APC tanada goyon bayan al’ummar Bichi kaso 90 cikin 100 sun gansu da jam’iyyar day an takarata kuma suna bata goyon baya da sukesa ran da izinn Allah zata kai ga nasara tun daga matakin shugabancin kasa,Gwamna yan majalisun jaha dana tarayya.

Exit mobile version