Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Al’ummar Birnin Suzhou Na Kokarin Cimma Burin Gudanar Da Rayuwa Mai Matsakaicin Wadata

Published

on

Bana muhimmiyar shekara ce wajen cimma burin gina zaman al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, kana samun galaba kan yaki da talauci a kasar Sin. A ra’ayin al’ummar kasar, menene zaman rayuwa mai matsakaicin wadata? Yaya za su yi domin cimma muradun?

Kauyen Yonglian na garin Nanfeng yana da nisan kilomita kimanin 100 daga birnin Suzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, wanda a da karamin kauye ne dake da mutane kadan, kuma tattalin arzikinsa a baya yake. Sakamakon manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ana kokarin raya sana’o’i, da mulmula karafa, da fadada fadin kauyen, al’amarin da ya sa ya zama daya daga cikin kauyuka mafi girma da yawan al’umma da karfin tattalin arziki a kudancin lardin Jiangsu.
Mazaunin kauyen, Zhang Zhiming, mai shekaru 75 a duniya, ya bayyana cewa, zaman rayuwarsa yana inganta kwarai da gaske, inda a cewarsa, a lokacin da bai samu isasshen abinci da gidaje masu inganci ba, amma yanzu ya samu kome kuma babu wani abun da zai dame shi.
Zhang ya kara da cewa, a halin yanzu, a kowane wata, baya ga kudin fanshon da ake ba shi, ya kan samu karin Yuan 900 daga kauyensa, al’amarin da ya gamsar da shi kwarai da gaske. (Mai Fassara: Murtala Zhang)
Advertisement

labarai