Al’ummar Dogon Dawa Sun Koka Kan Rashin Wutar Lantarki

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

A’ummar da suke garin Dogon dawa ta karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna sun shafe fiye da wata shida ba su  ga hasken wutar lantarki ba,wato suna zaune cikin duhu dundum ,na fiye da watannin da aka ambata.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa, rashin wannan hasken wutar lantarki ya sanya tattalin arzikin al’ummar yankin ya tsaya cik,musamman wadanda ke amfani da wasu na’urorin da ba sa tashi sai da hasken wutar lantarki.

A cewar wasu da wakilinmu ya zanta dasu sun ce a watannin baya sun yi karo-karon kudi,domin gyara na’urorin da suka lalace,da ya haifar masu da matsalolin da suke cik, amma tun da suka tara kudin ba wani ci gaba da suka samu.

Sun kara da cewar tun faruwar matsalar, sun tuntubi majalisar karamar hukumar Birnin Gwari, a nan ma alkawari aka yi ta yi masu,ba tare da an zo an ga halin kuncin rayuwar da suke ciki ba, haka dai suka sa wa sarautar Allah ido zuwa yanzu.

Wani mai magana da yawun al’ummar Dogon Dawa mai suna Malam Uwaisu ya ce hatta wasu manyan mutane a garin sun yunkura domin warware matsalar amma sun kasa saboda tsadar rayuwar da ake ciki a halin yanzu.

Exit mobile version