Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home AL'AJABI

Al’ummar Eggon: Yadda Suke Gane Kwartuwa Ta Hanyar Naƙuda

by Tayo Adelaja
October 6, 2017
in AL'AJABI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Ana Haihuwar ‘Ya Mace Suke Ɗaura Mata Aure

Daga Bashir Isah, Keffi

Tarihi ya nuna cewa al’ummar Eggon asali sun taho ne daga Ngazargamu, wato ƙasar Borno kenan a yau, daga nan suka ci gaba da tafiya har zuwa masarautar  Kwararafa. Bayan da aka tarwatsa Kwararafa ne aka ce suka tashi suka tsallaka Kogin Binuwai ta Ibi sannan suka warwatsu kana daga bisani suka yada zango a tsaunin Eggon a Jihar Nasarawa. Haka dai suka ci gaba da zama a kan wannan tsaunin sai bayan zuwan Turawa ne galibinsu suka sauko ƙasa.

samndaads

Eggon al’umma ce wadda ke da Sarki a matsayin shugaba, Aren Eggon daidai yake da Sarkin Eggon, shi ne aka naɗa domin ya jagoranci sauran jama’arsu. Kuma yanayin sarautar karɓa-karɓa ake yi a tsakanin manyan rassan ƙabilar su uku, wato Anzo da Eholo da kuma Eggon Ero. Yayin da majalisar da ke da alhakin naɗa sarki ita ce ake kira da ‘Malase Aren’. Majalisar da ke ɗauke da mutum goma sha biyu waɗanda baki ɗayansu jagorori ne a tsakanin al’ummar tasu. Bayan kammala komai ne sai su gabatar da wanda suka zaɓa a matsayin sarki ga ƙaramar hukumarsu.

Ta fannin al’adu kuwa, ba a amince namiji ya zo inda mace ke naƙuda ba, a kan samu wata ‘yar tsohuwa ce mai ilimin karɓar haihuwa ta zo ta yi aikinta na ungozoma. Amma idan ya zamana cewa mace mai shirin haihuwa ta shiga wani hali duk da ƙoƙarin ‘yar tsohuwar nan, a nan ne akan kira wani masanin magungunan gargajiya domin ya bada gudunmawarsa wajen ganin matar ta sauka lafiya.

Amma idan ta san cewa ta yi lalata da wani ƙato a waje baya ga mijinta sannan ta zaɓi ta bar wa cikinta ba tare da ta fallasa kanta ba balle kuma ta bada haƙuri, haka za ta ci gaba da shan baƙar wahala a naƙudar da take yi wanda a ƙarshe ma ta mutu ba tare da ta haife cikin da take ɗauke da shi ba. Saboda abin da gargajiyarsu ta haramta ne matar aure ta bada kanta ga namijin da ba mijinta ba.

Bayan mace ta haihu, haka za ta zauna a ɗakinta tare da abin da ta haifa na tsawon kwana bakwai kafin ta soma fita waje. Sannan idan namiji ne aka samu, za a bai wa jaririn kwari da baka alamar cewa zai zama sadauki ko kuma wani fitaccen mafarauci kenan a rayuwa. Wasu lokutan har da fartanya akan bai wa yaron wanda ke nuni da cewa zai zama hamshaƙin manomi da zai ciyar da iyalansa yadda ya kamata.

Idan kuwa mace ce, haka za a tara mata kayayyakin amfani na gida da suka haɗa da na girki, na tsabtace muhalli da sauransu, da zummar wai idan ta girma ta kasance mai kula da miji da kuma muhalli yadda ya kamata a matsayinta na mace a cikin al’umma. Duka waɗannan abubuwan kan gudana ne bayan dattawa sun yi wasu addu’o’i gami da ‘yan tanade-tanaden da gargajiyarsu ta umurta a yi ga abin da aka haifa.

Da yake Eggon mutane ne masu martaba kaciya ga yara maza, wannan ya sa a al’adance idan lokacin kaciya ya yi, sukan tara duk yara maza da suka kai shekara goma da haihuwa a yi musu kaciya a rana guda. Bayan an sha yaran sun warke, akan shirya musu ƙwar-ƙwaryan biki don faranta musu. Duk bayan shekara uku suke aiwatar da yin kaciya a tsakanin ‘ya’yansu maza amma ga waɗanda suka shekara goma da haihuwa.

Al’adar al’ummar Eggon ce idan yara maza suka cika shekara goma sha biyar da haihuwa, sai a haɗo kawunansu a tafi da su wajen bauta domin gabatar da su cikin harkokin addininsu na gargajiya da ake kira da suna Ashim. Akan buƙaci iyayen yaro da su bada, walau akuya ko kaza da kuma giya domin bikin shigar da ɗansu harkar addinin nasu. Yayin wannan biki kuwa, ba a yarda kowane yaro ya halarci wurin ba face waɗanda lamarin ya shafa kaɗai.

Batun aure a wannan ƙabila kuwa, a iya cewa tun ranar gini, ranar zane. Domin kuwa, yadda al’adarsu ta shimfiɗa shi ne cewa, idan aka haifi yarinya ba tare da ɓata lokaci ba akan ayyana wanda za a haɗa su aure idan sun girma. Wannan ne ma ya sa aka ce ba kowace mace ya kamata ta taɓa jinin mai haihuwa ba sai wadda ta kasance akwai dangantaka ta jini a tsakaninta da mai haihuwar. Bayan iyaye sun shaida wanda aka sanar da sunansa a kan za a haɗa su aure da jaririyar idan dukkansu biyu suka kai minzili, haka za a ci gaba da sanya musu ido tare da aiwatar da duka abubuwan da gargajiyarsu ta gindaya, musamman ma daga ɓangaren namijin zuwa ga yarinyar da ma iyayenta. A ƙalla shekara guda kafin auren, haka saurayin zai yi wa iyayen yarinya hidima ta hanyar haɗa kan abokansa a tafi gonan iyayen yarin a zabga musu aiki da dai sauran abubuwan kyautatawa.

Bayan iyayen yarinya sun gamsu da dukkan abin da surukin nasu ya yi, sannan ne za su yi masa sammaci tare da sanar da shi cewa an ba shi auren wance. Dagan an saurayin zai tafi ya shammaci yarinyar a duk inda ya ganta kawai sai ya sungume ta sai gidansu, shi kenan aure ya tabbata. Su kuwa iyayen yarinya a wannan lokaci, idan suka ji shiru ‘yarsu ba ta dawo gida ba sun rigaya sun san abin da ya faru. Bayan haka ne sai kuma  a shiga biki.

Game da sha’anin binne mutum idan aka yi mutuwa, kusan salon duka ɗaya ne a tsakanin jama’ar Eggon. Ma’ana, yanayin turbuɗe gawa a rami duk ɗaya ne ga mata da maza sai dai wasu ‘yan bambance-bambancen da ba a rasa ba. Alal misali, idan wani jagora a wajen bauta ya mutu yanayin janazarsa ya bambanta da na saura saboda ana ganin shi daban ne a cikin sauran jama’a. Suna da wasu zaratan mazaje na musamman da suke kira da suna ‘Makpngibi’ waɗanda aikinsu shi ne haƙar kabari a duk lokacin da aka yi mutuwa.

Bayan dodon da ya saba bayyana a lokutan da aka yi mutuwa ya gama nasa aikin, sannan ne za a tafi da gawa a saka cikin kabarinta tare da fuskantar da ita Gabas wanda a yaƙininsu nan ne mafarin mutum. Idan gawar namiji ne, bayan an saka shi a rami sukan yi masa matashi da hannunsa na dama, mace kuwa a yi mata da hannunta na hagu. Haka dai za a ci gaba da zaman makoki tare da aiwatar da abubuwan da gargajiyarsu ta umurta a yi.

Ahogben shi ne sunan da suke kiran Mahallici da shi, wanda suka yi amannar cewa Shi ne mahaliccin kowa da komai kuma masanin komai, haka ma yana ko’ina kuma yana aikata komai sai dai cewa ya yi nesa da bil-Adama wanda hakan ya sa mutane ke mu’amala da shi ta hanyar da suka kira da suna ‘Ashim’ ko kuma ta wata hanya daban. Sai dai, sun fi maida hankali kan abin bautar da suka alaƙanta shi da ƙarƙashin ƙasa saboda a cewarsu, shi kan sanya su samu amfanin gona mai kyau da dai sauransu. Baya ga Ashim, akwai sauran abubuwan bauta na al’ummar Eggon da suka haɗa da Akuk da Gango da Yamba da kuma Arikya.

Eggon, ƙabila ce da ta shahara da harkar noma matuƙa, inda sukan noma amfanin gona iri daban-daban. A taƙaice dai, noma shi ne babbar sana’arsu.

Sai dai yana da kyau a sani cewa, da tafiya ta yi tafiya, yanayin zamani da kuma harkokin addinai sun haifar da sauye-sauye da yawa a yanayin rayuwar al’ummar Eggon, ta yadda wasu al’adunsu na gargajiya an yi watsi da su domin a tafi daidai da zamani.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

TASKIRA: Amfanin Karas Da Dankali (Ɗan Hausa)

Next Post

Zargin Karɓan Na Goro: Ɗan Sanda Ya Kashe Mutum Biyu, Ya Rasa Ransa

RelatedPosts

Abba Kyari Nawa!

Abba Kyari Nawa!

by Sulaiman Ibrahim
10 months ago
0

Abokina ne da dukkanin ma’anar aboki, majibin lamurrana da dukkanin...

Hello world

by Leadership Group
2 years ago
0

Amfani Ruman Ga Lafiyar Dan’adam

by Sulaiman Ibrahim
2 years ago
0

Shi dai itacen ruman a turance ana kiran sa da...

Next Post

Zargin Karɓan Na Goro: Ɗan Sanda Ya Kashe Mutum Biyu, Ya Rasa Ransa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version