Khalid Idris Doya" />

Al’ummar Gabchiyari Sun Koka Kan Tsaikon Aikin Hanyarsu

OLYMPUS DIGITAL CAMERA

Sarkin Gabchiyari a cikin karamar hukumar Darazo, Malam Mohammed Garba ya gabatar da koken jama’ar kasar sa wa gwamnatin jihar Bauchi na bukatar gaggauta kare gina hanya mai tsawon kilomita goma sha biyu wacce ta tashi daga Darazo zuwa Gabchiyari cikin jihar wacce gwamnatin ta farko har zuwa yanzu aikin yaki ci ya kuma ki cinyewa.

Sarkin ya bayyana cewar, jama’ar garin Gabchiyari suna kuka akan aikin hanyar sosai, suna masu nuni da cewar, aikin hanyar yana tafiyar hawainiya, al’amarin da suka danganta shi da sakacin dan kwangilar da yake gudanar da aikin hanyar, wacce suka nuna rashin gamsuwarsu kan tafiyar aikin da baida wani tsawo sosai.

Malam Mohammed Garba ya yi tuni da cewar, hanyar wacce take da dimbin tarihi, idan aka kammala aikinsa za ta taimaka wajen fito da amfanin gona daga lungu-lungu, sako-sako na wannan yanki, har-ila-yau ta bunkasa tattalin arzikin yankin da ma na jihar Bauchi baki daya.

Ya ke cewa, “Amfanin wannan hanya yana da yawa a cikin karamar hukumar Darazo wadanda suka hada da zirga-zirga tsakanin mutane da fito da amfanin gonaki da kuma bunkasa safarar dabbobi, dadai sauransu”, in ji Sarkin.

Ya ce garuruwa da kauyuka da za a amfana da wannan hanya idan an kammala aikinta sun hada da Gamdumi, Baburi, Dollol, Kaigamari, Kohli, Taura, Malala, Garin Jauro, Gadom Jaurin Yamma, Wurohuna, Larabawa, Bille, Tsangaya, dadai sauransu.

Sarkin ya ce batun hanyoyin safara batutuwa ne da suke bukatar kulawan gwamnati saboda gudumawar da suke bayarwa, musamman wajen bunkasa tattalin arzikin kasa dana jama’ar ta, musamman kamar jaha irin ta Bauchi wacce kashi saba’in da biyar na al’ummarta suka dogara akan aikin noma.

Sarkin ya ce yankin na Gabchiyari yana daya daga cikin yankuna da suke ciyar da karamar hukumar Darazo, jihar Bauchi, dama kasa baki daya da abubuwan da suke nomawa da dabbobin kiwatawa.

Daga karshe, Sarkin ya bayyana fatar su na ganin gwamnatin tasa ido dan ganin samun nasarar kammala aikin hanyar da ta tashi daga cikin garin Darazo zuwa garin Gabchiyari, kuma ta hada da wassu daga cikin cikin yankunan Gombe da Bauchi.

Ya nemi gwamnatin jihar ta ji kukan jama’an yankin nasa domin a samu kammala musu aiyukan.

 

Exit mobile version