Haruna Akarada" />

Al’ummar Gama Sun Koka Kan Rashin Kammala Rijiyoyin ‘Inconclusive’ A Kano

Idan ba a manta ba, a watan Maris din da ya gabata ne, , Jihar Kano ta samu kanta a wani yanayi na dambawar siyasa, wanda wasu ke ganin cewa wannan ne karo na farko a tarihin Jihar da ta taba  shiga irin wannan yanayi. Wannan dambarwa kuwa, ta afku ne sakamakon zaben Gwamna aka yi, ake kuma zargin cewa, akwai kura-kurai da dama a ciki. Wadannan dalilai ne suka sanya Hukumar zabe ta Jihar Kano, ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba (Inconclusibe), ta kuma sanya wata rana ta daban da za a sake aiwatar da wani zaben a wasu a wasu daga cikin Kananan Hukumomin Jihar da abin ya shafa.

Wannan dalili ne, ya sanya Gwamnati mai ci (APC), da kuma ta adawa (PDP), wadanda su ne kadai Hukumar zaben ta baiwa damar fafatawa a tsakaninsu, sakamakon yawan kuri’un da suke da su damar shiga wannan zabe. A daidai wannan lokaci ne, kowacce daga cikin wadannan Jam’iyyu da ke neman kuri’un da za su ba su damar kafa Gwamnati, suka yi ta faman yin alkawarurruka na musamman ga al’ummar wannan yanki ta Unguwar Gama, sakamakon dimbin al’ummar da ke zaune a yankin da kuma tarin kuri’un da ake sa ran samu daga wurinsu don kaiwa ga samun wannan nasara.

Sakamakon haka ne, al’ummar Unguwar Gama a halin yanzu ke kokawa tare da neman dauki ga Gwamnatin da suka sahalewa, ta samu nasarar kaiwa ga gaci. Haka nan, al’ummar Unguwar, sun bayyana cewa, babban dalilansu na sake zaben wannan Gwamnati shi ne, ganin yadda Gwamnatin ta yi amfani da damar da take da ita, a daidai wannan lokaci na inconclusibe, wajen samar wa da mutanen wannan yanki ayyuka raya kasa, wadanda suka hada da: samar da hanyoyi, baiwa mata jari, gudanar da aikin ido a Asibiti kyauta da kuma haka rijiyoyin birtsatsai kimanin guda goma sha daya a wannan yanki na Unguwar Gama.

Babu shakka, wasu daga cikin wadannan rijiyoyin birtsatsai, sun kammala wasu kuma har zuwa yanzu, suna nan ba a kammala su ba. Koda yake, mafi yawan wadanda aka fara samarwa, tuni an yin amfani da su a wasu guraren, domin kuwa, kimanin guda tara daga cikinsu ana dibar ruwa ana sha, amma akwai wasu guda biyu da Akarada ya yi tattaki domin gane wa idonsa.

Har ila yau, Auwalu Muhammad a-ci-cingam, ya shaida wa Wakilinmu irin halin da suka tsinci kansu, musamman a bangaren rashin wutar lantarki da kuma ta leko ta koma din da suka gani da idanunsu kuru-kuru. Ya ci gaba da cewa, dalilinsa na yin wadannan maganganu shi ne, daya daga cikin wadannan rijiyoyin birtsatsai, a kofar gidansa aka yi ta, sannan an riga an kammala ta tsaf, kadai abin da ya rage, a hada ta fara bayar da ruwa, amma da suka ji shuru suka bibiya, sai aka ce da su sai dai idan sun yarda a hada musu da wutar NEFA, in ji shi.

Jin haka ne, ya sa mutanen wannan Unguwar suka ce ba su amince ba, domin kuwa Gwamnatin Jihar Kano, ta ba da umarnin a hada wa kowa da wutar Sola. Amma dai har yanzu, shiru kake ji babu wani labara. Don haka, muna kira ga wadanda abin ya shafa, su yi kokari su kawo mana dauki, don kuwa maganar da ake yi yanzu, duk jarkar ruwa guda Naira hamsin muke saya, a cewar Auwalu.

Shi ma a nasa tsokacin, Sadik Inuwa, wanda guda ne cikin ‘yan Jamiyar P.R.P, ya bayyana irin gudunmawa tare da kokarin da suka yi wajen tabbatar da ganin wannan Gwamnati ta kai ga samun nasara. A fadin nasa, birtsatse da suka rage ba a kammala ba, su ne kamar na  layinsu ‘yan balangu da kuma layin Masallacin yara wanda aka ce za a sanya masa wutar NEPA muka ce baa mince ba.

Don haka, muna kira ga Gwamnatin Jihar Kano, da ta sani cewa, mu ne muka tsaya kai da fata a wannan Unguwa ta Gama, har Allah Ya ba mu wannan nasara, domin kuwa ni ina daya daga cikin mutanan PRP na wannan yanki. Sannan ya kamata Gwamnati ta sani cewa, har gori aka rika yi mana ana cewa, idan aka ci wannan zabe ba za a karasa mana wannan aikin ba, dalili kuwa, cikin kafatanin rijiyoyin da aka haka, babu wadda ta kai tamu sakamakon yawan ruwan da take da shi, ba kamar ta ‘yan nono ba, kamar yadda suke cewa idan ruwan ya taho, sai kuma ya tsaya, in ji shi.

Inuwa, ya kara da cewa, magana ta gaskiya ita ce, al’ummar wannan Unguwar ta Gama, ta dogara ne kacokan a kan ruwan rijiyar birtsatsai, saboda haka, lallai a zo a hada mana ita. Haka zalika, zuwan Mai girma Gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje wannan Unguwa, ya sa shi ma ya zama dan wannan Unguwa ta Gama kamar yadda ya fada da bakinsa, amma sai ga shi kuma ana nema a manta da mu, a cewarsa.

Daga nan ne kuma, Wakilinmu ya karasa zuwa Unguwar Kwanar Jaba, Layin ‘Yan Nono domin  gane wa idanunsa wadannan rijiyoyin birtsatsai guda biyu da ake ta faman korafi a kansu, har ma ya yi katarin haduwa da daya daga cikin mazauna wannan Unguwa, ya kuma yi nasarar jin ta bakinsa a kan wannan rijiya ta birtsatsai.

Kamar yadda Wakilin namu ya nemi jin ta bakin nasa, Muhammad Ahmad, ya bayyana cewa, a lokacin da aka kammala aikin wannan rijiya ta birtsatsai, bayanin da aka yi mana bayan an daura wadannan karafunan shi ne, za a zo a karasa daga baya. Tun dai wannan lokaci, bas u sake zuwa ba, idan ma wata matsala aka samu, ba su zo sun fada mana matsalar ba, na san dai lokacin da suka kammala wannan aiki, ruwa ya zo da karfin gaske, don har akwai wadanda suka diba suka kai gida, ni kaina na sha wannan ruwan. Saboda haka, kirana a nan shi ne, wadanda ked a alhakin karasa wannan aiki, su taimaka su zo su karasa mana don al’ummar wannan yanki su samu sauki.

Exit mobile version