Alummar Garin Ruwan Dorawa Sun Bukaci Dauki Daga Gwamnatin Jihar Zamfara

Al’ummar garin Ruwan Dorawa dake karkashin masarautar Banagan Maru, cikin karamar Hukumar Maru dake jihar Zamfara, sun yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawallen Maradun da atuna da su wajen bada mukaman siyasa.

Sarkin Malaman Abuja Dakta Muhammad Muhammad Alkwandawi ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattauanwa da ‘yan jarida a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Sarkin Malaman Alkandawu ya bayyana cewa, sun ji dadin jawabin mai girma gwamna Matawallen Maradun da ya yi a lokacin sanya hannu a kasafin kudi na wannan shekara inda ya bayyana cewa, kowace mazaba ta kansila akwai ayyukan cigaba da za’a yi mata kuma masu mukaman siyasa zababo da wadanda na zaba zasu sanya iyadanu wajan duba ayyuakan.

Said dai gashi mu a mazabar mu ta Ruwam Dorawa bamu da mai mukamin siyasa da ke wakiltarmu a jihar kodaya.

Akan haka ne Sarkin Malaman Abuja ya ke kira ga gwamna Matawallen Maradun ya taimaka ya ba daya daga cikin mutanan gari wani mukami ta yadda zai taimaki alummar garin, da kuma sanya idanu wajan ganin anyi aiki mai inganci da gwamnatin za ta yi.

Sarkin Malaman ya kuma yi kira ga gwamna Matawallen Maradun akan ya sanya kwamitin don binciken wadanda suka maida wani yanki na kasuwa Ruwan Dorawa, gidajensu da kuma wadanda suka yi gina akan babbantin Ruwan dorawa da da zai hade da Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

A karkashin Sarkin Malaman ya kuma jinjina wa Gwamna Matawallen Maradun da ya kawo zaman lafiya a fadin jihar ta Zamfara da fatan Allah ya cika masa burinsa na ganin ya maida Jihar Zamfara ta zamo kamar sauran jihohi.

Exit mobile version