Daga Sabo Ahmad, Bello Hamza.
A makon da ya gabata ne al’ummar garin Migoma tare da hadin gwiwar kungiyar yada manufar dan majalisa dokokin jihar Kaduna mai wakiltar gundumar Basawa da ke karamar hukumar Sabon-garin, Zariya, Muktar Isa Hazo, suka karrama shi da lambar yabo bisa ayyukan da ya kawo wa gundumar na raya kasa da ci gaban al’umma.
A jawabin da ya gabatar wajen bikin karramawar, shugaban kungiyar ta yada manufar danmajalisar Hamza Idris Jika, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa suka karrama shi, shi ne, su da yake ’yangida ne sun san waye danmajalisar, saboda haka ko lokacin da ya fito takara sun kasance tare da shi, kuma sun ji irin alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe, babban a bin da ya karfafa musu gwiwa na karramawar shi ne, yadda ya sauke da yawa daga cikin alkawuran da ya dauka, musamman aikin hanyar da tashi daga Milgoma zuwa Kwakwaren-manu, wanda aiki ne da al’ummar wannan yanki suka yi shekaru suna bukatar a yi musu, amma hakan ba ta samu ba, sai a wannan lokaci. Sannan kamar yadda ya ce, danmajalisar ya tallafa wa matasa wajen karo ilimi da koyon sana’o’i da sauran wadansu fannuka a rayuwa don samun ci gaba.”Saboda haka, muka ya dace mu nuna yabawarmu ga danmajalisar bisa wannan tagomashi da yake yi mana a wannan yanki, shi ne ya sa muke karrama shi a wannan guri a halin yanzu, wanda kuma nan ce mahaifarsa”.
Shi kuwa a nasa jawabin danmajalisar, ya nuna godiyar ga wadanda suka karrama shin, sannan ya ce, wannan karrama ta kara masa karfin gwiwar ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga al’ummarsa, sannan kuma ta kara fito masa da kyakkyawar dangantakar da yake da ita da a’ummarsa. Wannan ma ta sa danmajalisar yake cewa, dukkan wanda yake ikikrarin ba a maimaita mulki to rashin irin wannan dangantaka ce tsakanin sa al’ummarsa. “Ina alfaharin cewa, kullum ina tare da mutanena, ba na guje musu,ina kokarin biya musu bukatu daidai gwargwado, saboda haka maganar maimaita wa ba na haufi, da yardar Allah za mu kasance a kundin tarihi da za mu karya wanna tsinuwa. Domin ni a gurina tsinuwa ce ke sa a kasa maimaita wa.
Taron ya samu halartar sarakuna da masu unguwannin yankin da sauran al’ummar da ke fadi wannan mazaba.