Connect with us

RIGAR 'YANCI

Al’ummar Kabo Na Alhini Da Jimamin Rasuwar Abba Salisu

Published

on

Al’ummar Garin Kabo sun shiga cikin alhini da jimami na rashin daya daga matasan yankin wanda ya rasa ransa a sakamakon hadarin mota da ya rutsa dashi akan hanyar Kano zuwa Gwarzo a ranar Lahadi data gabata 14/06/20.

Matashin wanda dalibi ne dake karatu a Jami’ar Bayero ta Kano da yake matakin aji na uku “300 Level” dan Shekaru 23 da haihuwa mai suna Kabiru Salisu Kabiru Kabo da akafi kira da Abba dane ga shugaban karamar hukumar, Hon.Kabiru Salisu Kabo.
Jama’a dai da dama sun yaba da irin kyawawan halaye na marigayin, dalibai daga jami’ar ta Bayero rukuni-rukuni ne da sauran jama’a daga sassa daban-daban ne suka halarci garin na Kabo dan yin ta’aziyya bayan jana’iza da akayi masa a makabartar Kabo.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: