Al’ummar Kaduna Sun Fara Barci Da Ido Biyu – Yaro Mai Kyau

An bayyana cewa, a halin yanzu al’ummar Jihar Kaduna sun fara bacci da ido biyu,  musamman yadda harkar tsaro ya kara inganta fiye da lokutan baya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai baiwa  Gwamnan Jihar Kaduna shawara akan harkokin Matasa,  Alhaji Auwal Yaro Mai kyau,  a yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna.

Auwal Yaro Mai kyau ya kara da bayyana  cewa,  a ‘yan  kwanakin baya al’ummar Jihar Kaduna sun fuskanci matsalar sara-suka,  wanda aka fi sani da ‘yan shara,  wanda hakan ta haifar da zaman dardar a tsakanin al’umma mazauna cikin garin kaduna.

A cewar Yaro Mai kyau,  “cikin yardar Allah,  a halin yanzu mun sami saukin wannan lamari ta hanyar fito da wani shiri na musamman wanda muke bin irin wadannan matasa muna zama da su,  muna nuna masu  irin illar da ke tattare da harkar sara-suka.  Saboda  mun fahimci cewa,  mafi yawancin irin  wadannan matasa suna aikata wannan mummunar ta’asar ne a dalilin  rashin aikin yi.”

Auwal Mai kyau, ya kara da cewa, “ Wani babban abin takaici shi ne,   mun lura da cewa mafi yawa daga cikin irin wadannan matasa sun kasance tamkar abokan ‘yan sanda,  domin da zarar an kama su ba za su dade ba sai a  sake su,  saboda irin daurin gindin da suke da shi wajen jami’an tsaro.  Sannan wasu da damansu kuma,  idan an kama su an  kai su gidan yari,  maimakon ace sun shiryu, a’a,  sai ma ka ga sun kara lalacewa fiye da yadda suke a da.”

“Wannan dalili ne ya sanya a karkashin gudummuwar mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna,  Malam Nasiru El-rufai,  muka yanke shawarar cewa,  a maimakon a rinka kama wadannan matasa a na zuwa ana kullewa,   maimakon idan sun fito su kara yin hankali,  a’a,  sai ma dai  harkar sara-sukar da suke aikatawa  ya fi na da,  domin abin ya riga ya zame masu jiki.   Saboda haka ne muka fito da wani shiri domin tallafa ma irin wadannan matasa ta hanyar ba su jari,  da  koya masu sana’o’in hannu wanda za su dogara da kansu,  sannan mukan  zabi  masu kwazo wanda suke da shinfida mai kyau na karatu  daga cikinsu,  muna mayar da su makarantu domin su ci gaba da karatunsu,  saboda mun lura da cewa mafi yawan wadannan matasa rashin aikin yi da galihu ne ke sanya su aikata irin wadannan munanan dabi’u.”

Sannan ya kuma kara da cewa, “ a bangare daya kuma,   binciken da muka gudanar,  mun gano cewa,  ba komai ke haddasa  irin wadannan harka ta  sara-suka ba, illa mummunar gabar da ke tsakanin ‘yan wancan unguwa da wannan unguwa. Kuma wani abin takaici shi ne, dan abin da ke haifar da irin wannan gaba na sara-suka da kasha-kashen mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba,  bai wuce rigima a kan Mace ba,  ko gardama a kan  kwallo,  ko kuma wani abu makamancin hakan.”

“Amma yanzu Alhamdulillah, za mu iya cewa komai ya kawo karshe,  saboda an sami saukin irin wannan ta’asa fiye da yadda suke a baya.  Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo cikin garin kaduna da kewaye.  Kawai yanzu abin da ya rage mana shi ne,  matsalar masu garkuwa da mutane a hanyar fita wajen garin kaduna,  wanda shi ma cikin yardar Allah, da hadin gwiwan jami’an tsaro an kusa shawo kan matsalar,  domin idan ku ka lura kullum asirinsu kara tonuwa ya ke yi, kullum kara kama su ake yi.”

Daga karshe,  Alhaji  Auwal Yaro Mai  kyau,  ya kara janyo hankalin Iyayen Yara, da su kara sanya ido a kan tarbiyar ‘ya’yansu.  Domin a cewarsa,  ice tun yana danye ya ke tankwaruwa,  amma da zarar an bar shi ya bushe shikenan, kuma lamari ya riga ya lalace sai gyaran Allah.

 

 

 

Exit mobile version