Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari Sun Yaba Da Ayyukan Hon. Garba Datti Babawo

Sabon Gari

Daga Nasiru Adamu,

Yau kimmanin makonni biyu kenan da Danmajalisar tarayya dake wakiltar shiyar zariya Hon. Garba Datti Babawo ya gaiyyato wasu shahararrun likitoci masana cututtuka daban daban, domin bada tallafi ga marasa lafiya ga al`ummar mazabar sa.

Wannan shine karo na 4 da dan majalisar ya bada irin  wannan talllafin, domin ragewa al`ummar tasa wahalhallun cututtukan da suke fama da  su yau da kullum a wannan yankin.

Malam Abdullahi Tukur dake hayin dogo Samaru na daya daga cikn mutanen da suka ci moriyar shirin, ya baiyyanawa wakilin mu cewar ya yi fama da ciwon kaba kimani shekaru 3 ya faskara sammun naira dubu 45  da za a yi masa aiki, sai gashi cikin nudufin Allah tare da jinkansa,  ya sa wannan  bawan Allah mai tausayin talakawa  ta dalilinsa ya sami biyan bukata. Daga bisani Malam Abdullahi ya yi kira ga shauran yan siyasa irinsa, su dauki halaiya irin ta Hon. Garba Dattii   Babawo domin al`umma su sami saukin rayuwa. Ya kuma yi wa Danmajalisar fatar cimma dukkan buri nasa na alkairi.

Shima a nashi jawabin da ya gabatar Malam Dalhatu Harunna, bayan sati biyu da samun nasarar warakar  tiyatar ciwon ido, wanda a halin yanzu  yake gani sarai, ya baiyyanawa wakilin namu cewar bai taba moran romon dimokoradiya ba sai a wannan lokacin wanda arayuwar sa bazai taba mantawa da ita ba.

Ita ko Hajiya Fatima Ishak wadda aka dorata akan magungunan hawan jini da ciwon siga, ta baiyyana cewar saukin da take samu a halin yanzu bata taba samun irinsaba, sama da shekaru 6 da  kamuwarta da wadannan cututtukan.

Wakilin mu bai yi kasa  a gwiwaba  sai da ya yi kokarin ganin daya daga cikin na hannun damar Hon. Garba Datti, watau Hon. Adamu (A.D.O.),wanda kuma shine  babban Sakataren Jamiyar APC na  karamar hukumar Sabon gari, domin karin haske abisa irin wannan aiki da Dan majalisar ke yiwa alummar wannan yanki, sai yabaiyyana mana cewar.

Baya ga aikin taimakon marasa  lafiya da wannan bawan Allah ya ke yi , Hon. Babawo bai  yi kasa a gwiwa ba wajen samarwa da alummar tasa ababen more rayuwar, kamar ingantacen ruwan sha gyaran makarantu hanyoyi, dakunan shan magani  da  kumma samarwa da matasa aikin yi, da ya hada da kasuwanci koyar da sanaa , bada tallafin karatu a manyan  makarantu na cikin gida da waje. Hon. Bbabbawo ya wadata mazabar sa da manyan ´´Transfomomi masu  daukar nauyin wutan lantarki 5000mg sama da 50 a yankin Sabon gari da kewaye.

Hon A D O ya ci gaba da cewar shi  bai taba ganin cikakken dan siyasa wanda ya damu da alumarsa, ba kamar Garba Datti Babawo, domin kuwa duk da kasan cewarsa a irin wannan matsayin kowanne lokaci wayarsa a bude take domin jin koken al umma, wanda irin haka ya wuyata ga sauran manyan yan siyasa irinsa.

Haka nan yace a halin yanzu mun shafa mun duba kowanne rukuni mutane tun daga kan yara, da  manya, matasa, gajiyayyu, maza ko mata ba wanda bai  ci gajiyar wannan bawan Allah ba injishi.

Daga karshe ya yi kira ga alummar gundumar Sabon gari, tare da shauran alummar kasarnan baki daya da su ci gaba da aduar fatan Allah ya yiwa kasarnan togomashi da shuwagabani masu  tausayin alummar su irin yadda Hon. Garba Datti Babawo yake yi.

Exit mobile version